Hukumar Hisbah da ke da alhakin dabbaka kyawawan dabi’u bisa koyawar addinin Islama a Jihar Kano, ta kama wasu mutum biyar da ake zargi da luwadi.
Shugaban Hukumar, Harun Ibn-Sina da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama mutanen da ake zargi a Unguwar Sheka da ke Karamar Hukumar Kumbutso ta Jihar.
- Buhari zai gana da duk Sanatoci 109 a daren Talata
- Majalisa ta ki amincewa da Onochie zama Kwamishinar INEC
Cikin sanarwar da Ibn-Sina ya fitar a ranar Litinin, ya ce wasu mazauna yankin ne suka shigar da korafi a kan wannan batu.
“Duk wadanda ake zargin sun haura shekara 20 kuma mun kama su ne a ranar 11 ga watan Yuli yayin wani simame na musamman da jami’anmu suka kai,” a cewarsa.
Ibn-Sina ya yi godiya ga mazauna yankin da sauran masu da ruwa da tsaki a harkokin tsaro da suka bayar da gudunmuwa wajen kama mutanen.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, Ibn-Sina yana bayyana takaicinsa kan matasan da aka kama da wannan zargi mai munin gaske.