✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta kama karuwai 44, kwalaban giya 684 a Jigawa

Hukumar ta ce har yanzu haramcin sha da sayar da giya na nan daram a Jihar.

Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa ta ce ta kama karuwai 44 tare da kwace kwalaben giya 684 a fadin Jihar.

Kwamandan hukumar a Jihar, Ibrahim Dahiru Garki ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da manema labarai a ofishinsa.

Ya ce an yi kamen ne a cikin mako biyu tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro a garuruwa 17 na wasu Kananan Hukumomin Jihar.

Ya ce, “Mun kama karuwai 44 da masu sayar da giya uku da kuma katan 57 na giyar yayin aikin.”

Kwamandan ya ce tuni hukumar ta damka mutanen ga hannun ’yan sanda domin a fadada bincike, kafin a mika su kotu.

Hukumar dai ta ce an kai samamen ne bisa umarnin gwamnatin Jihar na rufe dukkan wuraren sayar da giya da sauran wuraren badala a Jihar.

Sai dai ya ce har yanzu haramcin sha da sayar da giya da sauran miyagun kwayoyi na nan daram a Jihar.

Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da taimaka wa hukumar da muhimman bayanan da za su kai ga kama masu kunnen kashi.