✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta kama Al-Ameen G-Fresh a Kano

Hukumar ta kama shi kan yi wa Alƙur'ani Mai Girma izgilanci.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama fitaccen mawaƙin gambara kuma ɗan TikTok, Al-Ameen G-Fresh kan zargin yi wa Alƙur’ani Mai Girma izgilanci.

Hisabh ta kuma zarge shi da yin kalaman batsa a shafukan sada zumunta.

Gidan rediyon Freedom da ke Kano, ya tabbatar da kama G-Fresh.

G-Fresh dai ya yi ƙaurin suna musamman a kafar TikTok, inda da yawan lokuta kalamansa ke yamutsa hazo.

Idan ba a manta ba, tun bayan naɗa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin shugaban Hisbah da gwamnatin Kano ta yi, hukumar ta ƙaddamar da shirin yaƙi da baɗala a jihar.

Hisbah ta yi kamen masu yawon ta zubar a jihar, lamarin da ya haifar da cece-kuce musammam ga wasu da ke ganin hukumar ba ta bin ƙa’ida wajen gudanar da ayyukanta.

A baya dai Hisbah ta gayyaci G-Fresh kan dambaruwar aurensa da tsohuwar matarsa, Sadiya Haruna.

G-Fresh ya auri Sadiya Haruna, amma ba su jima ba, auren ya ɓaɓe, lamarim da ya kai su har ga kotun Musulunci a jihar.

Anjima ana kai ruwa rana kan batun auren nasu, amma daga ƙarshe G-Fresh ya sauwaƙe wa Sadiya Haruna, bayan ta biyasa diyyar Naira 500,000.