Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta cafke matasa 40 da ke aikata badala a fadin birnin jihar.
Kwamandan Hisbah a Jihar, Dokta Harun Ibn-Sina ne, ya bayyana a ranar Talata cewa 28 daga cikin matasan mata ne, sai kuma maza 12.
“Wadanda ake zargin, an cafke su ne tsakanin 27 zuwa 28 ga wan Yuni da misalin karfe 10 na dare a Karamar Hukumar Albasu, suna yada badala da karuwanci.
“Wasu daga ciki an cafke su ne a yankin digar titin jirgin kasa, unguwar Ja’en, Titin Gidan Zoo da sauransu,” a cewarsa.
Ibn-Sina ya ce hukumar za ta kara gudanar da bincike, duk wanda aka gano karon farko da aka kawo su ofishin Hisbah ke nan, za a yi musu afuwa a mika su ga iyayensu, ragowar kuma za a kai su kotu.
Ya jadadda cewar aikata badala laifi ne karkashin shari’ar Musulunci wadda jihar ta ke amfani da ita, sannan ya shawarci matasa da su ji tsoron Allah a kodayaushe.
A baya-bayan nan, hukumar ta Hisbah ta gargadi masu aikata laifuka a jihar cewa za ta ci gaba da yi musu hukunci ba sani ba sabo.