Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama akalla mutum 648 da ake zargin mabarata ne a titunan daban-daban na garin Kano daga watan Fabrailu zuwa yanzu.
Mai magana da yawun hukumar, Lawan Ibrahim, ya ce wadanda ake zargin an kama su ne a titunan Bata da Murtala Muhmamed da Asibitin Nasarawa da hanyar jirgin kasa da kuma Titin Yahuza Suya a cikin garin Kano. Mata 416 ne da kuma maza 232 aka kama.
- Aminu Ado Bayero ne kadai Shugaban Majalisar Sarakunan Kano
- Babu wanda rikicin Kudancin Kaduna bai shafa ba -Agwai
Ibrahim ya ce hukumar za ta ci gaba da kama masu bara da suka ki bin dokar hana bara da gwamnatin ta saka.
“Za mu tabbatar da hana bara a titunan Kano.
“An kuma tantance wadanda aka kama, haka kuma wanda aka samu laifinsu ne na farko za a mika su wajen ‘yan uwansu.
“Wadanda kuma suka saba yi za mu kai su kotu”, inji shi, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na NAN ya ruwaito.