Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana kama mutum takwas maza da mata da take zargi da satar waya da sauran manyan laifuka a masallacin Al-Furqan da ke unguwar Nasarawa a Kano.
Babban Kwamandan hukumar na Kano, Harun Ibn Sina ne ya tabbatar da kama matasan ga ’yan jaridu ranar Talata.
- Ban ga amfanin rufe iyakokin Najeriya ba – Shehu Sani
- Buhari zai yi buda-baki da su Tinubu a fadarsa ranar Talata
Ya ce wadanda ake zargin an kama su ne da yamma yayin da suke shan kwaya da sauran kayan maye a kusa da masallacin.
Ibn Sina ya alakanta wannan dabi’a ta matasan a matsayin wacce ta sabawa addinin Musulunci, musamman a watan Ramadan.
A don haka yayi kira ga al’umma da su sa ido tare da kai rahoton duk wani wanda suka gami suke kuma zargi da aikata ba daidai ba ga hukumar.
Ya ce Hisbah ba za ta yi kasa a guiwa ba a aikinta na tsaftace Kano daga dukkan abin ki.
A karshe ya ce za su mika wadanda ake zargin ga hukumomin da suka dace domin daukar mataki.