Wani samame da jami’an Hukumar Hisba suka kai kauyen Kudai da ke Karamar Hukumar Dutse, sun yi nasarar kama wani matashi da suke zargi da boye mata yana lalata da su da kuma sayar wa matasa kayan maye.
Matashin mai suna Adamu Usman Kudai an kama shi da kan zargin boye wata mace mai suna Fatima Ibrahim Jos.
Kwamandan Hisba na Jihar Jigawa, Malam Ibrahim Dahiru Garki ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun kama wanda ake tuhumar da kananan kwalaben giya da sholisho 186 kuma za su gurfanar da shi a gaban alkali.
Da yake bayani ga manema labarai Adamu Usman ya ce abin da Hisba take zarginsa da aikatawa gaskiya ne, inda ya ce Fatima budurwarsa ce kuma duk abin da ake zargi ya aikata da ita haka ne kuma ya kara da cewa yana shan sholisho gudu uku a rana, sannan ya sha kwalbar giya daya saboda ya samu nishadi.
Da take nata jawabin, Fatima Ibrahim cewa ta yi ta samu kanta ne a wani hali a rikicin Jos, wanda ya yi sanadiyar mutuwar iyayenta da mijinta inda a sakamakon haka ne ta tsinci kanta a matsayin ’yar gudun hijira kuma tana da yaro daya da ta haifa da mijinta. Amma yanzu haka tana da wani dan wanda ta samu a bariki ba ta hanyar aure ba.
Ta ce ta kasance a wani gida take kwana a Kasuwar Sara, tana yin karuwanci saboda ta ciyar da ’ya’yanta, inda suka hadu da Adamu ya dauko ta kawo ta Kudai ya ce wai zai aure ta, amma a karshe ya shiga lalata da ita.
Kuma ta nuna takaicinta game da halin da ta tsinci kanta a ciki kuma tana rokon al’umma su taya ta da addu’a kuma tana son wanda zai taimaka ya aure ta domin ya rufa mata asiri.
Sakamakon karuwar ayyukan badala a Jihar Jigawa, Hukumar Hisba ta yi wani taron gaggawa a hedkwatarta a jihar domin kawo karshen al’amarin.
A yayin taron da aka yi, kwamandan ya hori jami’ansa su tsaya tsayin daka wajen aikinsu sannan su guji yin aiki da son zuciya, kuma su zamo masu nuna babu sani ba sabo wajen gudanar da aikinsu domin duk wanda ya taka doka su kama shi kuma duk wanda suka kama ya taka doka su dauki matakin shari’a da shi komai matsayinsa.
Ya kara da cewa za su fara kai samame wuraren da ake aikata badala a fadin jihar da nufin kama batagari a duk inda suke. Sannan ya ce suna nan a kan bakansu na hana shan da sayar da giya a fadin Jihar Jigawa.