✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hirar karshe: Wasiyyata ga ’yan Najeriya —Bashir Tofa

Idan har na kammala rubuta wannan littafin to ni fa burina ya cika. Ko da na tafi shi ke nan.

Kwana 16 da suka gabata ne Aminiya ta samu zarafin tattaunawa da marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa, a filinta na TUNA BAYA.

Tsohon dan takarar Shugaban Kasa a Jamhuriyya ta Uku, kuma dan kasuwa marubuci, ya bayyana abubuwa da dama da suka shafi rayuwarsa da yadda za a gyara Najeriya da sauran batutuwa da dama da suka hada da burinsa na karshe a duniya duk a wannan tattaunawa da ita ce ta karshe da ya yi da kowace kafar labarai a duniya:

Tarihinka

An haife ni a Jihar Kano a 1947. Na fara karatu a Makarantar Firamare ta Shahuci daga nan na tafi Gwale na yi karamar sakandare.

Bayan na kamamla na je babbar sakandare ta Rumfa. Ban ci gaba da karatu a nan ba, sai a 1968 da aka nada marigayi Alhaji Ado Bayero a matsayin Jakdan Najeriya a Sudan, sai mahaifina ya hada ni da shi ya ce mu tafi in yi karatu a Sudan.

To da yake akwai mutanen Sudan da suke karantarwa a nan Kano a makarantu irin su Makarantar Nazarin Harshen Larabci da Addinin Musulunci da aka fi sani da (S.A.S.) da Kwalejin Abdullahi Bayero (yanzu Jami’ar Bayero) su kuma suka tuntubi wani Farfesa El-Tayyib, wanda ya samo min gurbin karatu a Jami’ar Khartoum, don haka muka tafi a watan Oktoba.

Da muka isa Khartoum sai muka tarar ashe su tun watan Yuli suke fara shekarar karatunsu don haka dole sai da na jira zuwa badi ke nan.

Daga nan sai na fara aikin wucin-gadi a ofishin Jakadancin Najeriya da ke birnin Khartoum.

A wannan lokaci na rubuta wani littafi mai suna ‘Jagoran Alhazai’ wanda na bi sawun duk hanyoyin da alhazan Najeriya suke bi tun daga gida zuwa Maiduguri zuwa Chadi har su isa Sudan sannan su tsallaka ta tashar jirgin ruwa ta Sudan (Port Sudan) zuwa Jiddah.

Kuma na hada da masu zuwa a jirgin sama su tashi daga Kano su sauka a Jiddah. Ina zaune a Sudan sai na ga cewa idan ambasada ya kammala aikinsa a Sudan ba zan iya zama har shekara biyar a Sudan ba tunda karatun likita zan yi.

Sai na fada wa mahaifina cewa ni ba na so in zauna a Sudan har tsawon wadannan shekaru. In zai yarda ina so a samo min wata makaranta a wani wurin, sai ya ce to in nemo da kaina a dukinda nake so.

Sai kuwa na samo makaranta a Birmingham da ke Birtaniya, sai ya biya min kudin makarantar. Na baro Sudan a watan Agustan 1969 na tafi Birtaniya.

Da na isa sai na sake yin jarrabawar A Level a Cambridge daga nan sai aka kawo takardar zaben jami’ar da za ka shiga, akwai sunayen jami’o’i guda biyar ka zabi daya, kawai sai na zabi Jami’ar Birmingham tunda a can nake da ma, sai na cike cewa zan karanta likitanci.

Lokacin da sakamako ya fito sai aka kai ni sashen nazarin jikin dan Adam, sai na ga malami da wata adda a hannunsa yana sassara gawa, sai na ce yanzu wannan abin zan yi? Sai aka ce ai shi ne karatun, ai kuwa take na suma sai da aka zuba min ruwa na farfado.

Sai na ce to wannan karatun ba da ni ba. Duk da yake a sakandare muna yin darasin halittu, amma a wancan lokacin mu kwado muke fedewa ba mutum ba.

Don haka sai na rasa yadda zan yi saboda duk sauran jam’i’o’in ma likitanci na cike, don shi kadai nake so, saboda tun sakandare abokaina suke kirana Dokta Bashir don sanin yadda nake son fannin.

Daga baya dai na samu gurbi a wata jami’ar a nan dai Birtaniyar inda na karanta fannin tattalin arziki da kasuwanci a nan na samu na kamamla digirina na dawo Najeriya.

Aminiya: Bayan ka dawo wane aiki ka fara?

Da na dawo mahaifina ya tambaye ni abin da nake son yi. Sai na ce ni ba zan yi aikin gwamnati ba, kasuwanci nake sha’awa.

Sai ya tura ni wajen Alhaji Ibrahim Dankani, abokinsa ne da kullum suke tare. Da na je sai Alhaji Ibrahim Dankani ya ce to, abin da zan fara fada maka shi ne duk abin da ka koyo na boko a Turai ka ajiye shi a gefe, ka shiga kasuwa ka ga yadda ake kasuwanci a aikace, ba abin da kake karantawa a littafi ba.

Saboda idan ka dogara da abin da aka koya maka a littafi, to, ba za ka yi nasara ba, amma idan ka fara a aikace sai ka dauko wanda suka koya maka a littafi ka hada su, sai ka fi samun nasara, don mu ba abin da yake a littafi muke yi a nan ba.

To da yake tun a lokacin mahaifina yana sayar da motoci da wasu kayayyaki da yake rarrabawa daga kamfanoni, sai na fara wannan harka kafin in koma gefe in fara nawa na kaina.

Da farko na fara da sayar da dardumai da shimfidun daki da sauran kayan kawata gida.

Daga baya na shiga sayar da askirin inda nake raba wa masu kekuna suna yawo a gari da kararrawa suna sayar wa jama’a. Na kuma taba bude wajen wankin tufafi.

Don tsarin da na yi a sana’ar wanki abin sha’awa ne, misali kowane yanki yana da alamar da ake sanyawa a jikin kayan da aka kawo daga can, kamar a ce shudi alama ce a jikin kayan mutanen Gwagwarwa, sannan da motoci na rarraba wadannan kaya.

Abin ya fara kamar gaske, saboda da na sayo injinan a Turai sai da na kawo Turawa suka zauna wata uku suna yi wa ma’aikatana horo har suka kware, amma dai abin bai dore ba.

Amma dai darasin da na koya shi ne irin wadannan sana’o’i ya kamata a ce mutum ya yi da kansa, ko ya zauna a wurin yana kula da abin da yake gudana.

Rashin yin wannan ya jawo wadannan sana’o’i da na yi sun durkushe.

Ni ban san halin mutanenmu ba, na dawo daga Turai da irin tunanin can. Shi ya sa duk wanda ya zo ya ce min yana so zai yi kasuwanci sai in ce to ka zauna ka yi da kanka, idan ka dora wani ka koma ka kwanta to ka gama yawo.

Aminiya: Su wa za ka iya tunawa daga wadanda aka taso tare da su?

Gaskiya da yawansu sun rasu, amma dai akwai irin su Alhaji Salisu Bayero da dan uwana Alhaji Fa’izu Baffa da Alhaji Muhammad Labbo da Alhaji Ahmad Aminu Yola da tsohon Minista Alhaji Shamsuddin Usman.

A Ingila kuma akwai irin su Alhaji Bello Bayero da Alhaji Mukhtar Dangana da Alhaji Abubakar Rimi da y a zo daga baya.

Aminiya: Yaushe ka fara siyasa?

Ai tun a Ingila na fara shiga siyasa, domin ni ne Jami’in Walwala na Daliban Najeriya a Birtaniya, kuma ni ne na ba da shawara aka kafa Kungiyar Dalibai ’Yan Asalin Jihar Kano a Birtaniya, wadda muka sa Alhaji Bello Isa Bayero, Shugaba.

Abin sha’awa shi ne yadda Gwamnatin Kano a karkashin Alhaji Audu Bako ta karbe mu hannu bibbiyu, don ko dalibai za a nema wa guraben karatu, to mu ake tuntuba sai mun tantance jami’o’in da kwasa-kwasan da za su karanta sannan za a turo su.

Ga kudi har Fam dubu da Gwamna Audu Bako yake ba mu duk shekara don mu yi walimar karshen shekara.

Wannan ya sa mun shahara sosai don duk fadin Birtaniya ba walima kamar tamu, har tambaya ake, wai yaushe ’yan Kano za su yi walimarsu.

Wani abin sha’awa da daukacin dalibai suka yi a lokacin Yakin Basasa shi ne muka samu Alhaji Sule Kolo, Jakadan Najeriya a Birtaniya muka ce masa mun sadaukar da alawus dinmu na wata daya ga sojojin Najeriya don ba su kwarin gwiwa.

Bayan mun dawo Najeriya a 1975. Sai a 1977 zamanin Gwamna Kanar Sani Bello na tsaya takarar kansila da wani kawuna a Dawakin Tofa, kuma na samu nasara na tafi majalisa.

Lokacin kuma da maganar siyasa ta kankama sosai, sai muka kafa kungiyoyi daga jihohin Arewa, ana haduwa ana taro ana tattauna yadda za a bullo wa harkar.

Mu daga nan Kano muka zabi Farfesa Ibrahim Umar ya wakilce mu a tarurrukan da ake yi, sai ya zama akwai shugabanni guda biyar, su ne: Alhaji Shehu Shagari da Farfesa Iya Abubakar da Alhaji Adamu Chiroma da Mista Sunday Awoniyi da kuma Madakin Kano Alhaji Shehu Ahmad, aka yi taro a Kano aka samar da wata kungiya mai suna National Movement of Nigeria, wadda Alhaji Ibrahim Tahir (Talban Bauchi) yake Sakatare.

Daga nan aka yi ta neman jama’a har daga Kudu, aka kuma canja mata suna ta koma NPN inda na zama Sakatarenta na farko.

Da aka zo fid da dan takarar Shugaban Kasa sai ya zama mutum biyu ne suka fi yawan kuri’a, Shagari da Danmasanin Kano, sai na samu Dan masanin Kano wanda babana ne, na ce masa ranka ya dade gara ka janye wa Shagari saboda ko an shiga zabe shi ne zai ci, sai sauran manyan jam’iyya suka yarda a kan hakan, don haka ya karbi abin magana ya sanar da janyewarsa.

Daga nan aka yi zabe marigayi Alhaji Shehu Shagari ya zama Shugaban Kasa. Ni ma a wannan lokaci na ci Sakataren Kudi na Kasa na NPN.

Sai dai ban yi aikin nan ba saboda lokacin da kuruciya sai na fara rubuce-rubucen takardu da mukalu ina cewa ba wanda ya isa ya ci kwabon jama’a a kyale shi, ko wane ne shi.

Sai wadansu suka ceto fa wannan yaron ba ya da kunya don haka suka yi abin da suka yi na bar mukamin.

Aminiya: Yaya aka yi gwagwarmaya a Jamhuriyya ta Uku?

Lokacin da Shugaban Kasa Janar Babangida ya sanar da za a yi siyasa sai dukkanmu tsofaffin ’yan NPN muka hadu a Kaduna don kafa sabuwar jam’iyya.

Amma sai na sanar da su cewa ni ba zan yi tasu ba, amma zan nemi wadansu samari mu kafa tamu, shi ne muka samar da Liberal Convention.

Wata rana ina gida sai Janar Abdulsalam ya kira ni ta waya ysanar da ni cewa an zabi kungiyarmu za a yi mata rajista.

Amma daga baya sai duk aka narke a cikin NRC, wadansu kuma suka shiga cikin SDP.

Da aka zo taron jam’iyya na kasa Allah Ya jikan Sarki Ado Bayero, shi ya kira ni ya ce ya kamata in mayar da hankali tunda mutane sun ce ni suke so. Hakan ya sa na shiga takara har aka kai ga yin zaben Yunin a 1993.

Abin da ya faru a bayyane yake, cewa an yi zabe sannan aka soke shi, kuma wallahi har kawo yanzu ba wanda ya sanar da ni dalilin da ya sa aka soke zaben.

Aminiya: Duba da yadda al’amura suka tabarbare tun daga kan rashin tsaro, cin hanci da rashawa, rikicin siyasa da na kabilanci da suke faruwa a kasar nan, a ganinka ta yaya za a bullo wa wadannan al’amura don samun gyara?

A ra’ayina idan har ana so a samu gyara a kasar nan, to dole a samu canjin shugabanci. Wallahi idan ba a samu sabon tsari ba, to, babu wani canji da za a samu.

Canjin nan kuwa zai samu ne tun daga kan jam’iyyun siyasa har zuwa kan mutanen da suke jan ragamar shugabancin.

A canja mutane sababbi wadanda aka tabbatar suna da nagarta wadanda za su iya, amma in har wadannan mutanen za a yi ta juyawa, to, haka za a yi ta tafiya ba tare da samun canjin da ake bukata ba.

Matasa su fito masu ilimi su nemi takarar dukkan mukamai.

A ajiye wancan Gwamnan da ya yi mulki sau biyu yana so kuma ya dora yaronsa ko sanatan da ya yi sau uku shi ma a jiye shi a gefe a zuba wadansu sababbi. A gwada wadansu mutanen domin a ga kamun ludayinsu.

A yi watsi da wadannan shirmen APC da PDP. A ajiye mutanen da suka dade suna mulki a gefe. Gwamnan nan da ya yi sau biyu a jiye shi sanatan nan da yake ta yi, shi ma a ajiye shi a gefe.

A samu wadansu sababbi a zuba su a mulkin. Babu wani abu na kwarai da ke samuwa cikin sauki. Don haka akwai bukatar ’yan siyasa su fito su yi kokari su samar da mutane nagartattu wadanda za su kai al’umma ga tudun-mun-tsira.

Amma ba wai a zauna a yi ta surutu na neman sauyi ba tare da daukar mataki ba. Ya kamata matasa su dawo daga rakiyar ’yan siyasar da ke dora su a hanyar lalacewa.

Su yi kokari su kawar da kansu da zuciyarsu daga kwadayin abin da suke samu daga hannun wadannan ’yan siyasa su tsaya su yi abin da ya dace wajen mara wa nagartattun mutane baya don zama shugabanni nagari.

Idan ban da ma wauta ta yaya za ka rika yaba wa barawonka? Mutumin da ke satar dukiyarka shi ne kuma gwaninka?

Akwai bukatar ku yi karatun ta natsu ku daina bin wadannan mutanen suna ingiza ku kuna dabancikuna kashe junanku a banza a duniya, sannan idan kun je Lahira ku hadu da azabar Allah.

Mu a nan Kano kokarin da muke yi ke nan insha Allah haka za mu yi don mu samu sauyi, amma fa hakan ba za ta yiwu ba, sai mutane sun jajirce sun sadaukar da kansu domin jihadi za a yi. Mu sani canji bai taba samuwa cikin sauki.

Matasa muna fada musu wannan lokaci nasu ne idan ba su tsaya sun yi abin da ya dace ba, to, fa sai sun gwammace gara jiya da yau.

Su kau da kansu daga kwadayin abin da wadannan shugbannin suke ba su, su tsaya tsayin daka wajen ganin an samu canji mai inganci.

Amma idan har suka zama ’yan Allah Ya ba ku mu samu to fa abubuwa ba za su yi kyau ba.

Aminiya: An dade ana maganganu a kan yadda za a magance harkar barace-barace a Arewa, mene ne ra’ayinka a kai?

To a wancan lokacin da aka fara barace-barace mutane ba su da yawa, kuma akwai zuciyar taimako. Amma yanzu da aka yi yawa sai abubuwan suka hargitse.

Ban da wannan kuma zuwan Turawa ya mayar da karatun Kur’ani mara makoma a tsarin hukuma, wanda ba haka abin yake a baya ba.

Don haka wajibi ne a samar da wata hanya da masu karatun addini za su rayu kamar kowa. Dole sai an samu gwamnati mai kishi da za ta samar da makarantun Alkur’ani da yi musu tsari kamar yadda aka yi wa ilimin boko.

Amma ban da sata ba abin da ake yi a gwamnatin. Idan ka dauki kudin da ake sata, babu irin makarantar da ba za a iya gyara ta ko gina ta ba.

Aminiya: Kasancewarka marubuci yaya kake kallon dabi’ar al’ummarmu ta rashin son yin karatu?

Ni a gaskiya a ra’ayina mutanenmu suna son yin karatu sai dai ba su da kudin sayen littattafai shi ya sa ba su yi.

Domin kuwa a duk lokacin da na buga littattafaina ba a iya sayensu amma da zarar na fito ina raba su kyauta, kada ku ga yadda mutane suke rububin karbarsu.

Da farko da na fara harkar wadansu mutane sun gwada karbar har na Naira miliyan hudu za su sayar, amma abin bai yiwu ba, don wadansu ma har yanzu da ake magana ba su dawo da littattafan ba, kuma ba su dawo min da kudin ba.

Kuma akwai lokacin da Jami’ar Ahmadu Bello ta karbi littattafan amma haka suka gama zamansu a makarantar ba a saya ba.

Aminiya: Wane littafi masu karatu za su sa rai da fitowarsa nan gaba?

Zuwa yanzu na rubuta littattafai 14 wadanda kuma na buga su wadanda suka hada da Kammaninka Tunaninka da Kimiyyar Sararin Samaniya da Rayuwa Bayan Mutuwa da Aikin Hajji da Jagora Ga Masu Son Kafa Kwamitin Unguwanninsu da Kai Ma Ka Dara da sauransu.

Amma a yanzu akwai littafin da nake rubutawa mai suna ‘Mutane Da Wurare A Duniyar Islama’ Ina shafi na 740.

Abin da nake yi shi ne ina dauko sunayen mutane da suka yi rayuwa a wurare daban-daban a duniyar Musulunci ina dan rubuta dan gajeren tarihinsu. Ina bincike a wasu littattafai, ina zakulo sunayen mutanen. Yadda na tsara littafin na biyo jerin haruffan ABCD yanzu dai ina kan harafin U. Insha Allah na kusa kammalawa.

Wannan littafi ya tsaya min a rai saboda na gaza kammala shi. A koyaushe na ji rashin lafiya ta kama ni sai in ce shi ke nan ba zan kammala littafina ba ke nan?

Wallahi kullum rokon Allah nake Ya bar ni in kammala rubuta wannan littafi. Idan har na kammala rubuta wannan littafin to ni fa burina ya cika. Ko da na tafi shi ke nan. Ni wallahi shi kadai nake jira in kammala.