Marigayi Alhaji Bashir Tofa, shi ne dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NRC zaben ranar 12 ga watan Yunin 1993, inda ya fafata da dan takarar SDP, marigayi MKO Abiola.
Alhaji Bashir, wanda dan siyasa ne, dan kasuwa kuma marubuci, ya rasu da sanyin safiyar ranar Litinin, uku ga watan Janairun 2022, kuma an binne shi a makabartar Sansanin Alhazai da ke Kano.
- Hadimin Buhari ya yi wa Kwankwaso ‘maraba da dawowa APC’
- Tsohon dan takarar Shugaban Kasa, Alhaji Bashir Tofa, ya rasu
Ga wasu abubuwa 18 da ya kamata ku sani a kan marigayin:
- An haife shi a Kano a ranar 20 ga watan Yunin 1947, kuma asalin iyayensa ’yan kabilar Kanuri ne.
- Ya fara karatu a makarantar Firamare ta Shahuci da ke Kano, sannan ya wuce makarantar City Senior Primary School, ita ma a Kano.
- Ya halarci Kwalejin Provincial da ke Kano tsakanin 1962 zuwa 1973.
- Bayan kammala karatu, ya fara aiki da kamfanin inshora na Royal Exchange Insurance daga 1967 zuwa 1968.
- Ya halarci Kwalejin City College da ke Landan daga 1970 zuwa 1973.
- Ya fara siyasa ne a 1976, lokacin da aka zabe shi Kansila a Karamar Hukumar Dawakin Tofa.
- A shekarar 1977, an zabe shi dan majalisa.
- A jamhuriya ta biyu, ya rike mukamai daban-daban, ciki har da Sakataren NPN an Jihar Kano, Sakataren Kudi na jam’iyyar na kasa da kuma mamba a Green Revolution National Committee.
- A jamhuriya ta uku, yana cikin wata kungiya da ake kira Liberal Movement, wacce ta rikide zuwa Liberal Convention, ko da yake ba a yi mata rajista a matsayin jam’iyya ba.
- Ya shiga jam’iyyar NRC a shekarar 1990.
- A 1993, ya lashe tikitin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NRC, inda ya doke Pere Ajunwa da Joe Nwodo da kuma Dalhatu Tafida.
- Mataimakinsa a takarar shi ne Sylvester Ugoh, dan kabilar Igbo, kuma duka su biyun mambobin rusasshiyar jam’iyyar NPN ne.
- Ko da yake ba a fitar da sakamakon zaben ba, amma alamu sun nuna cewa ya sha kaye a hannun Abiola.
- Tofa kuma dan kasuwa ne, mai kwarewa a harkar mai da kuma masana’antu.
- Shi ne Shugaban kamfanin IPEC da kuma Abba Othman and Sons.
- Yana kuma cikin mambobin hukumar zartarwar kamfanonin Impex Ventures da Century Merchant Bank da kuma General Metal Products ltd.
- Ya wallafa litattafai har guda takwas a harshen Hausa da suka hada da Tunaninka Kamanninka da Kimiyyar Sararin Samaniya da Kimiyya da Al’ajaban Al-Kur’ani da Gajerun Labarai da Amazadan a Birnin Aljanu da Amazadan da Zoben Farsiyas da Rayuwa Bayan Mutuwa da kuma Mu Sha Dariya.
- Ya rasu yana da shekara 75 a Kano, kuma an yi jana’izarsa a gidansa da ke unguwar Gandun Albasa, sannan aka binne shi a makabartar Sansanin Alhazai da ke Kano.