✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hijirar ’yan bindiga daga Zamfara zuwa Katsina ta tayar da kura

Wasu rahotannin da ke fitowa na cewa daruruwan ’yan ta’adda a karkashin jagorancin wani dan bindiga mai suna ‘Starnational’ sun taso daga Jihar Zamfara zuwa…

Wasu rahotannin da ke fitowa na cewa daruruwan ’yan ta’adda a karkashin jagorancin wani dan bindiga mai suna ‘Starnational’ sun taso daga Jihar Zamfara zuwa wasu yankunan da ke tsakanin kananan hukumomin Safana da Batsari da ke Jihar Katsina.

Al’ummar yankunan da abin ya shafa sun ce ’yan ta’addar na tserewa daga farmakin da sojoji ke kai masu a Zamfara.

Taskiya da Runka da Gora da Labo da sauransu na cikin garuruwan kananan hukumomin biyu da aka ce ’yan bindigar sun yada zango.

Mazauna kauyukan sun ce, ’yan ta’addar sun hada kai da wani dan bindiga mai suna Usman Modi-Modi wanda ya addabi mazauna yankin.

Har ila yau, al’ummar sun ce ’yan ta’addar suna da yawa kuma dauke da miyagun makamai, suka koma wadannan yankuna tare da shanu da sauran dabbobi masu yawa, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Akalla ’yan bindigar sun kai mutum dubu, wasu daga cikinsu a kan babura kusan 300 sun kwana a kauyen Labo ranar Asabar da ta gabata.

Wata majiya mai tushe ta ce, ’yan ta’addar sun raba kansu a akalla kauyuka biyar da ke gefen dajin Rugu da ke tsakanin Karamar Hukumar Safana da Batsari da kuma wani bangare na Jihar Zamfara.

Sai dai majiyar ta ce, abin da ba a sani ba shi ne ko ’yan bindigar na kan hanya ne ko kuma sun kafa wasu sababbin sansanoni ne a yankin.

Mutanen kauyukan sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da sauran hukumomin tsaro su gaggauta hana ’yan ta’addar duk wata dama da za su iya gudanar da ayyukansu.

Fitaccen dan ta’addar nan Dankarami da ’yan dabarsa sun shahara wajen kai harehare a kauyuka da garuruwa a Jihar Zamfara da Katsina.

Wani mazaunin daya daga cikin yankin da ’yan bindigar ke kokarin mamayewa ya ce, “Tuni wasu daga cikin mutanen kauyen sun fara yin kaura domin gudun fadawa cikin bala’in da ke tafe.

“Akwai bukatar sojoji su tura jami’ansu na kasa da na sama domin kakkabe ’yan ta’addar kafin su fara barna.”

Rahotannin da ke fitowa daga garin Runka na Karamar Hukumar Safana da ke iyakar dajin Rugu na nuna cewa a makon jiya, an ga wadannan ’yan fashi suna share ciyayi don yin matsuguni, wanda hakan ke nufin suna son zama dindindin ne.

“Mun ji cewa Dankarami ya zo wurin Usman ModiModi kwanakin baya, kuma Modi-Modi ya ba shi makamai.

“Hakan na nufin za su yi aiki tare don ci gaba da yin ta’addancin da suka saba a wadannan yankuna.”

Shi dai Dankarami kamar yadda wata majiyar ta ce, ya zo da miyagun makamai da mazauna yankin suka ce ba su taba ganin ’yan ta’addar da irinsu ba

Da aka tuntubi Alhaji Ibrahim Ahmad-Katsina, mai ba Gwamna Aminu Masari Shawara a kan Harkokin Tsaro a kan lamarin sai ya ce, “Jami’an tsaro ne kawai za su iya cewa wani abu a kan lamarin domin su suke da wannan hurumi.”

Shi kuwa kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, CSP Gambo Isah da aka tuntube shi sai ya ce, suna binciken sahihancin bayanin.

Sannan akwai irin wannan ayyuka na sojoji da ’yan sanda ke ci gaba da kai hare-hare a kan ’yan ta’adda a Zamfara, wanda yana tilasta wa wasu ’yan ta’adda komawa wasu sassan jihar.

“A nan Jihar Katsina, jami’an tsaro, musamman sojoji da ’yan sanda sun lura da hakan kuma suna gudanar da bincike don gano gaskiyar yadda abin yake tare da daukar matakin da ya dace,” in ji CSP Gambo Isa.