Kungiyar Hezbollah da ke kasar Lebanon ta ce mayakanta sun harba makamin roka kan hedkwatar hukumar leken asirin Isra’ila ta Mossad da ke kusa da birnin Tel Aviv a ranar Laraba.
Rundunar sojin Isra’ila ta yi ikirarin kakkabo wani makami mai linzami da Hezbollah ta harbo daga Lebanon.
An yi ta jin karar jiniyar gargadi a Tel Aviv, cibiyar tattalin arzikin Isra’ila, amma babu labarin ko an samu asarar rayuka ko jikkata.
An kuma kara jin karar gargadi a wasu yankuna na tsakiyar Isra’ila, ciki har da birnin Netanya.
- MDD ta gaza ɗaukar mataki kan yaƙin Gaza —Erdogan
- An sallami sojar da ta zargi shugabanta da neman lalata da ita
- DAGA LARABA: Dalilin Da ’Yan Najeriya Ke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi?
Kakakin rundunar sojin Isra’ila Nadav Shoshani ya ce ba zai iya tabbatar da manufar Hizbullah da harba makami mai linzami daga Lebanon.
A wannan mako ne sojojin Isra’ila sun kai hare-hare mafi muni a cikin shekara guda da ake gwabzawa.
Sun kai hari kan shugabannin kungiyar Hizbullah da ke samun goyon bayan kasar Iran da wasu daruruwan wurare a cikin kasar Lebanon.
Isra’ila kuma ta sake kai hare-hare ta sama a kudancin Labanon a kazamin fada mafi muni tsakaninsu a cikin shekara guda.