✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausawan Layin vagoviri sun kafa kwamitin tsaro

Hausawa mazauna Layin bagobiri da ke Kalaba a Jihar Kuros Riba  sun kafa kwamiti da zai rika yin aiki kafada-da kafada da jami’an tsaro da…

Hausawa mazauna Layin bagobiri da ke Kalaba a Jihar Kuros Riba  sun kafa kwamiti da zai rika yin aiki kafada-da kafada da jami’an tsaro da ke aiki a jihar domin wanzar da tsaro da kuma kare lafiyar mazauna unguwar Layin bagobiri ’yan kwanakin nan ya sha fama da yara zauna gari banza da suka kware wajen yi wa mutane sane da kwace da kuma a wasu lokutan ma bindiga suke tare mutum su nuna masa don ya razana su yi masa fashi. Lamarin da ya kai yaran kan rika tare hanyoyi da suka san na nesa   ka fito zuwa masallaci domin sallar asuba sa suka rika kara musu bindiga su mayar da su gida su yi masu kankat.

Ganin lamarin  na neman dagulewa m usu suka yunkuro suka fara yin taro na nemann shawara daga jami’an tsaro da a’lummar gari domin a samu mafita, ida taron  ya tara dimbin mazauna Kalaba aka shawarta yadda za a taru a fitar da jaki daga cikin dan duma.Unguwar Hausawa da ke layin bagobiri ta kasance daya daga cikin  babbar  cibiyar kasuwanci da ake yi a birnin na Kalaba ganin cewa al’ummar mazauna unguwar batagari na neman kawo masu cikas, sai suka ma kafa kwamiti kan yadda za a magance matsalar .

Aminiya ta samu sunayen shugabannin kwamitin mai suna zaman lafiya da tsaro  da hadin kai da kuma ci gaba, wato a Turance Peace Security,Unity and Progress. bayan da aka shawart a kuma bakuna suka zo daya nan take aka zabi Alhaji Ya’u Isma’il Girei shugaba, Alhaji Ibrahim Shehu mataimaki. An dai zabi Alhaji Salisu Abba Lawan Sarkin Hausawa a matsayin uban kungiya. Sauran masu mukami irin nasa da suka rufa masa baya su ne Assheik Malam bashir Salisu Abuga, babban Limamin Masallacin JIbWIS Kalaba da kuma Alhaji Sale Suleman Jimeta, kuma Alhaji Ali Abubakar Ancau  da barista Musa Abdullahi Maigoro mataimaki na musammna ga Gwamnan Kuros Riba kan harkokin baki  matsayin wakilin gwamna

Sauran mukaman su ne na sakatare Alhaji Sha’aban Abdullahi da  sakataren kudi  Alhaji Danlami Sale doss da Alhaji Hussaini Yakubu mataimakinsa. Alhaji Abdullahi Ibrahim “ba Guarantee”.matsayin ma’aji sai  Alhaji Muhammad Abbas “badarawa” matsayin mai binciken kudi, wato odita, mukamin jami’in hulda da jama’a da mataimakinsa an zabi Alhaji Nasiru Ishaka da Alhaji Nafi’u Musa .

Jim kadan da kammala zaben aka rantsar da su kuma kowa ya yi alkawarin yin aiki tsakanin sa da buwayi. Malam basher Abuga ya shawarci al’ummar Arewa mazauna  Kalaba da su hada kansu,  kuma da taimakekeniya da jin  tsoron Allah ne kowa yasan nauyin  amanar da aka dora masa. Ana sa rai kwamitin ya tunkari duk wata matsala ta tsaro idan ta taso bisa hadin kan jama’ar unguwar da kuma fallasa maboyar ’yan ta’addar da ke zama barazana ga unguwar.