✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausawan Kudancin Kaduna na neman El-Rufai ya yi musu masarauta

Al’ummar Hausawa a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna sun yi kira ga gwamnan jihar, Nasiru El-Rufa’i da ya kirkirar musu da sabuwar masarauta. Mutanen…

Al’ummar Hausawa a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna sun yi kira ga gwamnan jihar, Nasiru El-Rufa’i da ya kirkirar musu da sabuwar masarauta.

Mutanen yankin karkashin wata kungiya kare hakkin al’ummar yankin mai suna Cibiyar Na-Tanko ta ce Hausawan da ke kananan hukumomin Chikun, Kajuru, Sanga, Kauru, Kagarko, Zangon Kataf da kuma Lere na bukatar masarauta domin tabbatar da hadin kai da zaman lafiyar yankunan.

Jagoran kungiyar, Alhaji Aminu Idris da sakatarenta Yusuf Muhammad Yunus a wata sanarwa sun ce, “Al’ummarmu na ci gaba da mika kokon barar kirkirar sabuwar masarauta ga Hausawan Karamar Hukumar Chikun kamar takwarorinsu na wasu yankunan.

“Muna so mu bayyana karara cewa gundumarmu ba ta taba kasancewa karkashin yankin Kudancin Kaduna ba, kuma duk wani yunkuri na duk mai son cimma wata manufar siyasa ta hanyar shigar da kananan hukumomin Chikun da Kajuru yankin ba ya kan ka’ida saboda a Kaduna ta tsakiyar suke,” inji sanarwar.

Kungiyar ta kuma yaba wa kokarin gwamnan jihar da kantomar karamar hukumar ta Chikun, Hajiya Hadiza Ladi Yahuza kan abun da suka kira kokarin da su ke yi na ceto yankunan da ake wa danniya a jihar da kuma tabbatar da zaman lafiya.