An haifi Mogaji Nurudeen Basunu a garin Ibadan a 1967, kuma bai taba zuwa Arewacin Nijeriya ba. Yana magana da harshen Yarbanci da Larabci, amma ba ya iya yin magana da harshen Hausa ko Fulatanci.
Wannan haka yake, domin da yawa daga cikin iyalan gidan Basunu wadanda adadinsu ya kai 3,500 ba sa jin Hausa ko Fulatanci, duk da asalinsu ‘yan Jihar Katsina ne.
- An rufe SAHAD STORE kan yi wa kwastomomi zamba a Abuja
- ’Yan sanda sun cafke mai jinyar ’yan bindiga a Sakkwato
Amma akwai mata da yawa daga cikin iyalin da ke iya jin Hausa, amma ba a fayyace ainihin adadinsu ba.
Mogaji Basunu yana da matan aure Yarabawa guda 3, kuma babu daya daga cikin ‘ya’yansa 7 da ke jin Hausa.
Abinci
Abincin da ake ci a kasar Hausa na cikin jerin akansarin irin abincin da iyalin Basunu suka shaida cewa ana ci a gidajen Basunu, tun daga abincin da aka fi so, wanda ya hadar da Amala, wanda shahararren abinci ne na kasar Yarbawa da ake yi da garin albo, zuwa na kasa-kasa a jerin irin su Tuwo da Shinkafa, wadanda aka saba yi a kasar Hausa.
Aminiya ta samu Mogaji yana sanye da farin rawani wanda ya ya yi masa kyau, ya shaida mana na cewa, sarautar Mogaji ko shugaban iyali, dangi ne ke zabarsa, sannan sai babban limamin garin Ibadan ya nada masa rawani.
Tattaunawar tamu ta gudana ne a Zaure kuma tare da ’yan uwa da dama. Dukansu maza da mata sun sha ado cikin kaya masu kyau, kuma suna kamanceceniya sosai da Yarbawa ta fuskar sutura da magana da kuma salo.
Yarbawa
Mun yi amfani da yaren Yarbanci a mafi yawan hirar sai dai ‘yan wasu lokuta da a kan bukaci a yi fasara ko tafinta.
Haka kuma a lokacin hirar tamu daga lokaci zuwa lokaci ana tafka muhawara duk a cikin harshen Yarbanci a yayin da Mogaji Basunu da wasu mutane suka nemi karin haske a kan wata magana, daga nan kuma sai a ci gaba da hirar.
Akwai wasu ‘yar muhawara da aka yi a kan ko gine-ginen gidan ya samo asali ne daga Yarbawa ko kuma daga Hausawa ko kuma daga duka biyun.
Zaure
Zaure na taka rawar da ya saba takawa a kasar Hausa.
Binciken da aka yi a google ya nuna cewa, zaure kalmar Hausa ce da ke nufin ‘babban dakin karbar baki. Zauren gidan yana da girman da zai iya daukarmu duka.
Akwai baka uku a gaban zaure kuma an girke shi da ginshikai da suke rike da shi. Lokacin da iyalin gidan suke magana da harshen Yarbanci, suna fadar kalmar zaure ta Hausa, a yayin da ake magana a kan bangaren gidan.
Wannan wani abu ne na bakin kalmomi da ke suka samo asali daga harshen Hausawa na iyalin, wanda ya gushe, amma ana jin ragowar burbushinsa.
Usman Basunu Sa’ad Abubakar, Limamin Sabo Ibadan, ya yi magana game da dangin Basunu. Wannan na cikin hirar da aka yi da Hausawan Sabo Ibadan.
A cewarsa, Usman Basunu, wanda shi ne kakan gidan, ya zo Ibadan daga Jihar Katsina a karni na 19, ya zauna a can, ya zama babban limamin lardin Ibadan na farko, inda ya yi aure daga kabilar Yarbawa kuma – kusan shekara 200 baya – zuriyarsa ‘yan kabilar Yarbawa ne.
Yanzu an maye gurbin asalinsu na Hausawa ko kuma sun hade da Yarbawa, wanda hakan ya zama ruwan dare a yanayin zamantakewar Nijeriya.
Usman Basunu shi ne marubucin Teskiratl Kuritubiyat (Littafin da ya yi tsokaci kan yadda ake taimaka wa matattu) wanda aka rubuta a shekara ta 1850.
Asalin rubutun da sauran rubutun da Usman Basunu ya yi suna nan a wajen iyalinsa ko kuma danginsa.
Hausa
Dangin Basunu yana cikin Unguwar Ita Okoro, wani yanki na Oja’ba kusa da Fadar Olubadan na Ibadan, wato babban basaraken lardin Ibadan.
Kamar yadda iyalan gidan suka ambata a baya, Yarabawa magina ko masu sana’ar gini ne suka gina gidan, wadanda sana’o’in hannunsu ke nuna tushen Arewa a dangin Basunu.
Wannan ya bayyana abubuwa biyu da ke cikin ginin, yayin da wasu masu ziyara ke yi wa ginin kallon mai tushe na Hausawa, wasu na yi masa kalon gini ne mai tushen Yarbawa, wato gini ne guda da ke da fuskar al’ummomi biyu.
A yau, akwai gine-ginen Yarbawa da yawa a gidan, wadanda suka kunshi benen da aka yi daben samansa da katako.
Gidan iyali
Ginin gidan yana da Masallaci da kuma dakuna da yawa. Haka kuma ya kunshi benaye masu yawa da suke da matattakala da tagogi da zanen baka a kwance a jikin bango da kuma lunguna da yawa masu duhu.
Yanayin gine-ginen abu ne mai matukar ban sha’awa wanda ke nuni da lokuta da kuma irin yanayi na da.
Babbar hanyar zuwa gidan da kuma wani sashe ta hanyar da baƙo zai iya fita, duka suna da ban mamaki ta hanyoyi dabandaban kuma za su faranta wa duk baƙo rai a lokacin da ya iso gare su.
Yarbanci
Farfesa Idris Shaba Jimada na Sashen Tarihi na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, wanda ya kwararre ne a fannin nazarin tarihin zamani, ya yi tsokaci a kan kalmar ‘Yorubanised’ wato sauyuwa zuwa kabilar Yarbanci, “Wannan wani tsari ne na al’adu wanda ke faruwa cikin ‘yan shekaru kadan.
“Zuriyar mutumin da ya bar Katsina zuwa Ibadan a 1835, ya zauna a can, ba za su iya tunawa da Katsina ba, wato inda suka fito.
“Abubuwan da ke janyo hakan sun hada da gushewar harshensu na asali da kuma nisa daga garinsu na asali da kuma yiwuwar yanayi na sabon gidan da suke rayuwa a ciki.”
Farfesa Afis Oladosu, farfesa a fannin Larabci da addinin Islama a Jami’ar Ibadan, ya ce, wasu daga cikin malamai idan sun isa wani wuri, sai su daina yin hijira, su kama waje su zauna, su hayayyafa a yankin da suka zauna tare da yin aure da mazauna yankin kuma su raini ’ya’yansu a wajen.
Jajircewa
Ya ce, “wadannan malaman sun bar wurarensu na asali, wuraren jin dadinsu, inda suka je wuraren bincike da yada addini.
“Lokaci ne ko yanayi da sufuri ba shi da sauki, a lokacin ana amfani da jirgin kasa ne wanda bai wadata ba, lokacin da mutane ke tafiya a kasa ko kuma suna amfani da watakila doki ko raƙumi.
“Wasu daga cikinsu za su mutu a hanya, wasu kuma ba za su sake komawa gida ko ganin iyalansu ba.”
Sambo Eleruja
“A matsayina na masanin tarihi ban yi mamakin labarin Usman Basunu ba. Misalai irin wadannan suna da yawa a cikin tarihinmu.
“Bari in ba ku wani misali na musamman. Wannan shi ne labarin Malam Sambo Eleruja a garin Ogbomoso.
“Asalin wannan mutumin ya yi hijira ne daga Sudan a karni na 19. Ya sauka a takaice a Maiduguri. Daga nan ya koma Ogbomoso, inda sarkin garin ya ba shi masauki.
“Eleruja yana nufin mai daukar makamai. Wannan suna ya samo asali ne daga rikicin masu bautar gumaka da sauransu da wani malamin addinin Musulunci.
Ya yi amfani da hanyoyin Musulunci wajen fatattakar masu ibada ta gargajiya da matsafa. Shi ya sa suka kira shi Eleruja,” in ji Rasheed Olaniyi, farfesa a tarihin Afirka kuma shugaban Sashen Tarihi na jami’ar Ibadan, wanda ya gudanar da aikin bincike a kan kaura, dangantakar kungiyoyi da kuma siyasar ainihi.
Olaniyi ya yi karin haske a kan aikin Eleruja, inda ya ce, “Duk da kasancewarsa Musulmi, yana taimakon shugaba wanda ba Musulmi da musamman na kasar da Musulmi suka mamaye.”
Ya ci gaba da cewa “Misalin Mallam Basunu daya ne daga cikin gidaje da dama da ‘yan Arewa suka hade da Yarbawa.
“Abin da ya jawo sauyi shi ne batun hadin kai da kuma yadda mutane ke daraja inda suka zauna. Suna auratayya, kuma al’adu sun samu karbuwa a wajen malaman da suka zo.”
Kwanciyar hankali
“Akwai mutane da yawa daga Ogbomoso a Funtua, Jihar Katsina da suka zama Hausawa. Domin suna jin dadin inda suke zaune.
“Dangantakar da ke tsakanin Hausawa da Yarbawa dadaddiya ce. Mutane suna son inda suke da wadata, inda suke da kwanciyar hankali,” in ji shi.
A lokacin ziyarar farko da muka kai gidan dangin a watan Disamban bara, Mogaji ba ya gida. A ranar ziyarar wasu mutane sun zauna a cikin zaure, inda wata mata ta yi sauri ta dauko wayarta domin ta ba da lambar Mogaji.
Basunu
A kan ma’anar sunan Basunu, Mogaji Basunu ya bayyana cewa, “Ma’anar ba tana nufin mahaifi ba ne. Busunu sunan Sarki ne. Don haka Basunu yana nufin uban Sarki.”
Ya kuma yi bayanin “Basunu suna ne na gaske. Basunu dan Sarki ne a Katsina, Amma da mahaifinsa ya rasu ya kamata ya zama Sarki, amma sai aka nada kaninsa Muhammadu Awwal Sarki.
Wannan ta faru ne a 1833. Don haka, suka bar tsoho, aka nada karamin dan uwan a sarauta a lokacin. Saboda haka, a yanzu suna kiran dattijon Baba Oba, ma’ana suna ce masa uban Sarki ko Basunu.”
Ya fito daga wata masarauta ce a Jihar Katsina. Basarake ne daga cikin iyalan gidan sarauta, wanda kuma sunansa Usman Abubakar, inda ya kasance malamin addinin Musulunci,” in ji Ridwan Adebayo Basunu, malami a Cibiyar Larabci ta Nijeriya da ke Elekuro, Ibadan.
“Kafin ya yi hijira daga Katsina, dan uwansa ya riga shi barin Katsina, kuma ya zauna a Abeokuta ta Jihar Ogun, inda ya kasance Limami.
“Daya daga cikin dalilan da suka sa shi yada addinin Musulunci a Kudu shi ne dan uwansa ya riga ya yi hijira,” inji shi.
Uthman Basunu kwararre ne a fannin Fikihu da kuma nahawun Larabci.
1835
Ya ce, an haifi Usman Basunu a 1770 kuma ya bar Katsina a 1835 zuwa Ibadan, inda Olubadan Oluyole ya tarbe shi da kyau a lokacin.
Garin Ibadan ya fara ne a matsayin sansanin yaki kuma ya kasance tungar yakin basasar Yarbawa a karni na 19.
Ifa Oracle ya sanar da Olubadan cewa, Musulmi za su zo Ibadan sanye da rawani kuma mai martaba ya sanar da sarkin cewa ya tarbe su da kyau.
Musulmi za su taimaka wajen tabbatar da tsaro a Ibadan kuma birnin zai fadada, in ji shi.
A cewar Mogaji Basunu, “Mutane sun tuntubi mai suna Ifa oracle wanda shi ne dodon tsafinsu, wanda ya shawarci Oba Oluyole cewa wani zai zo daga nesa sanye da rawani dauke da sandar addini.”
Ya bayyana cewa, “Mai maganar ya fada wa Oba Oluyole cewa, idan mutumin ya zo Ibadan, ya zauna a nan, Ibadan za ta kasance cikin kwanciyar hankali kuma za ta fadada.
“Lokacin da Basunu ya sauka a Ibadan, sai suka nada shi a matsayin limamin Ibadan na farko.
“A lokacinsa ya yi addu’a ga lardin Ibadan. Idan sun tafi yaki zai yi musu addu’a kuma za su yi nasara. Za su kama bayi da sauran abubuwa Sun yi nasara a lokacin da suka tafi yaki.
“Ya kuma yi addu’ar birnin Ibadan ya fadada.”
An tabbatar da wannan bayanin ne ta hanyar bincike na google wanda ya bayyana Usman Abubarri Basunu, ‘Dan asalin Katsina ko Dindi’, a matsayin limamin lardin Ibadan na biyu daga 1839- 1871
Misali, Mogaji a nan shi ne Nurudeen. Nurudeen sunan Musulunci ne, Titilope kuma sunan Yarbawa ne. Wannan ya nuna cewa, mu Hausawa ne,” in ji Ibrahim Basunu a lokacin da yake karin haske a kan zaben sunayen a cikin iyali.
Dangane da tsarin gine-ginen gidan kuwa, Mogaji Basunu ya bayyana cewa, “Wannan gidan ‘yan kabilar Yarbawa ne suka gina shi, amma tsarinsa daga Arewa ne.
“Mai yiwuwa dan kwangilar da ya gina gidan Bayarabe ne, amma tsarin kwafin abin da ake iya samu na Arewa ne.
“Daya daga cikin ‘ya’yanmu mata tana karatu a Bauchi. Na ce mata ta rika sauraron abokan karatunta Hausawa domin ta yi koyi da su,” inji wani dan gidan.
Ginin kasa
Oladosu ya yi magana a kan gudunmawar da malaman addinin Musulunci suke bayarwa wajen gina kasa.
Ya ce, “Idan za a yi maganar tasiri ga kasa ko gina kasa, kana so ka tambayi malaman Larabci da na Islama nawa muke da su a Nijeriya a yanzu.
“Za mu iya yin magana a kan sashen farko na karatun Larabci da Ilimin Musulunci a Kudu maso Yammacin Nijeriya.
“An kafa sashen koyar da Ilimin Larabci da na Islama a 1962 kuma ta kai ga kafa wadancan jami’o’in da ake koyar da wadannan tagwayen darussa na Larabci da na Islama.
“Dukkansu sun ci gajiyar Ibadan kuma Ibadan ma ya ci gajiyar rubuce-rubucen wadancan malaman, wanda wasu ma har aka samar da farfesoshi ta hanyar rubuce -rubucensu ba ma a Nijeriya kadai ba, har ma a duniya baki daya”.
Hausa da Larabci
“Allah Ya tsare mu, Ya yi mana jagora. ’Ya’yanmu za su kara jin Hausa da Larabci a nan gaba,” in ji Mogaji Basunu yayin da hirar ke dab da karewa.
Da yake amsa tambaya game da tsagen da ke fuskarsa, ya yi murmushi, inda ya ce, alamomin Hausa-Fulani ne. Haka kuma ya bayyana bukatar da ke akwa ta inganta harshen Hausa a cikin iyali, wanda tushensu da asalinsu ne, inda suka sauya ta hanyoyi da yawa a cikin shekara 189 da suka gabata.