A ranar Larabar makon da ya gabata, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar karshen shekarar 2015 kuma ta farko irinta da wasu Wakilan kafofin yada labarai a fadar gwamnatin tarayya, Abuja, tun bayan da ya hau kan karagar mulkin kasar nan watanni bakwai da suka gabata. Batutuwan da Shugaba Buhari ya samu damar amsa wa sun hada da batun matsayin da tattalin arziki yake ciki, musamman sake karya darajar kudin kasar nan, wato Naira da yaki da cin hanci da rashawa da makomar janye sassaucin farashin man fetur da inda `yan mata Makarantar Sakandaren Chibok ta Jihar Borno suke ciki da `yan kungiyar Boko Haram suka sace yau kwanaki 634. Akwai kuma batun ware kudi har Naira biliyan 47.5 da aka ce `yan Majalisun Dokokin kasar nan sun yi don saya wa kawunansu motocin alfarma.
Ya kuma tabo dalilan da suka sanya gwamnati ba za ta saki tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara ba ta fuskar tsaro, wato Kanar Sambo Dasuki mai ritaya da Shugaban Gidan Rediyon Biafara, Mista Nnamdi Kanu da batun mai yiwuwa gwamnatinsa ta hana mata sa Hijabi, bisa ga irin yadda ta bayyana a baya-bayannan mata masu sanye da Hijabi su ake amfani da su wajen kai akasarin hare-haren da `yan kungiyar Boko Haram suke kaiwa a jihohin shiyyar Arewa maso Gabas da ma wasu jihohi na Arewacin kasar nan.
Akan batun yaki da cin hanci da rashawa, an ruwaito Shugaba Buhari yana cewa: “Zuwa yanzu mun yi nasarar kwato dubun dubatar miliyoyin Naira daga mutanen da suka sace kudin kasar nan, amma ba za mu iya bayyana ko su wanene ba, bare nawa muka kwato, kasancewar batun yana gaban kotuna, da muka mika musu shaidar mu, muna kuma zaman jiran yadda za ta ka ya.” In ji shugaba Buhari. Akan abin da ya sanya gwamnati ta ki sakin Kanar Sambo Dasuki da Mista Kanu, duk da kotu ta bayar da belin su. A nan shugaban kasar ya ce. “Muddin muka saki mutanen biyu suka tsallake kasar nan ba za su dawo ba, don laifuffukan da ake tuhumarsu da aikatawa manyan laifuffuka ne, inda ya kara da cewa shi Mista Kanu ma ana tuhumarsa da laifin kokarin juyin mulki, bisa ga irin shirye-shiryen da gidan rediyonsa ya ke yadawa.” Ta bakin Shugaba Buhari.
Shugaba Buhari kuma ya yi batun yiwuwar gwamnatinsa za ta hana mata sanya Hijabi, yana mai cewa. “Muddin aka ci gaba da kai hare-haren Boko Haram, to, kuwa ba makawa, za mu hana sa Hijabi,” ya kara da cewa, “Cusa munanan akidun kai hare-haren bama-bamai ya yi kamari. A duk cikin batutuwan da Shugaba Buharin ya tattauna da manema labaran, ba ni da aniyar duba martanin da `yan siyasa, musamman babbar jam`iyyar adawa ta APC, ta mayar, domin dama, jam`iyyar ta PDP, ta mayar da martani akan dukkan aikace-aikace ko wani tsari na gwamnatin tarayya ta APC, ya zama wajibi, wasu martanin ma na adawa ne kawai ba wai don sun cancanci ta mayar da martani akan su ba, da haka ita ma take sa ran ta karbi mulki daga hannun jam`iyyar ta APC, kamar yadda APC ta karba daga hannunta.
Ba aniya ta ba ce a wannan makala in yi magana akan irin martanin da jam`iyyar adawa ta PDP ta mayar ba, ko irin kura-kuran da shugaba ya tafka da yadda aka gabatar da tattaunawar, bare kuma bayanan da shugaban kasa ya bayar cikin amsa tambayoyin. Illa dai a kan batun aniyar gwamnatin na za ta iya hana mata sa Hijabi, muddin hare-haren bama-bamai da `yan kungiyar Boko Haram, suke kaiwa ya ci gaba. Tuni dai kungiyoyin addinin Islama irin su kungiyar kare hakkin Musulmi ta kasa, wato MURIC da Cibiyar wayar da kan al`ummar Musulmi ta kasa, wato MPAC da kungiyar Izala ta kasa baki daya. Daraktan MURIC, Farfesa Ishak Akintola, bayan ya yi tur da alllawadai da wannan aniya, ya kuma ce, bayan ana neman a labe da guzuma ne don harbin karsana, aniyar hana sa Hijabin zai iya bude kafar rudani a kasar nan. Ina mai nuni da cewa, idan har amfani da kayan Sarki da ake wajen kai hare-hare a kasar nan bai sa aka haramta amfani da su ba tsakanin jami`an tsaro, to, kuwa don me za a hana yin amfani da Hijabi.
Shi ma a cikin nasa martanin shugaban na Izala na kasa baki daya Sheikh Abdullahi Bala Lau, kira ya yi ga gwamnatin tarayyar da ko kusa ka da ta kuskura ta hana mata sa Hijabi, domin kuwa mata su sa Hijabi umurni ne na Allah SWT. A martanin Cibiyarsu ta MPAC, Malam Disu Kamor cewa ya yi, hana sa Hijabin ba abin da zai kawo sai kara tabarbarewar matakan tsaron, don kuwa in ji shi ba a gyara barna da abin da aka halatta.
Ina ga ya kamata in tunatar da Shugban kasa Buhari a kan abin da ya riga ya sa ni, na batun addini da yadda ya kamata ya rika yin takatsantsan wajen furta matsayin gwamnatinsa a kan al`amarin. A wannan lokaci da a kullum Allah Yake kara ba gwamnatinsa nasara cikin yaki da `yan kungiyar Boko Haram, ya ce gwamnatinsa za ta duba yiwuwar hana mata sa Hijabi, ba karamar fitina zai jawo kasar nan da gwamnatinsa ba daga Allah bisa ga la`akari da abin da Maluma suke cewa. Yin haka tamfar yin fito-na-fito ne da Allah, wajen neman karya dokokinSa. Har lokaci ya yi tsawo da Shugaba Bahari zai manta da irin carin da aka rika yi da shi a lokacin yakin neman zaben shekarar 2011, bisa ga jawabin da ya yi a Sakkwato a lokacin akan batun shari`a da aiwatar da ita idan har ya yi nasara. Kafin ka ce kwabo kungiyoyin mabiya addinin Kirista sun yi ca a kansa, suna zargin zai Musulantar da wadanda ba Musulmi ba muddin ya yi nasara a lokacin.
Ai ko a kwanannan jam`iyyyar adawa ta PDP ta zargi Shugaba Buhari da cewa, yana baya-baya da yin cudanya da mata, wanda PDP din take kokarin ta nuna tamfar kyamar matan yake yi, amma duk Musulmi da ya taso a cikin tarbiyyar Musulunci ya san haka ya kamata kowane Musulmi ya kasance, cikin harka da matan da suka haramta akan sa, balle kuma shugaba, amma tunda batu ne na siyasa, shi ma nan sai da ofishin shugaban kasar ya maida martani yana cewa, ko kusa shugaban ba ya dari-dari da mata, karshe ma dai a makon da ya gabata jaridu sun dauko hoton Shugaba Buhari, yana karbar bakuncin gamayyar mata `yan siyasar kasar nan. To don me ya ji tsoron wancan zargi, amma yanzu kuma yake kokarin afkawa cikin haddin Allah? Tun da dai a lokacin tsohon shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da ake fama da hare-haren Boko Haram, ba kakkautawa ba a ma maganar kawo karshen su bai yi gigin zai hana mata sa Hijabi ba? To, yanzu da gwamnatin Shugaba Buhari, har take sa ranar kawo karshen rikicin, ba ta da wani dalili da zai sa ta hana mata sa Hijabi. Don haka a yi hattara.
Hattara Shugaba Buhari: Ka da ka bata rawarka da tsalle
A ranar Larabar makon da ya gabata, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar karshen shekarar 2015 kuma ta farko irinta da wasu Wakilan kafofin…