✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hattara da fina-finan Hausa

Ina shawartar ma’abota kallon fina-finan Hausa da su san irin wadanda ya dace su rika kalla. Domin wasu fina-finai. Misali Jamilu Jidda da Kishiyar gida…

Ina shawartar ma’abota kallon fina-finan Hausa da su san irin wadanda ya dace su rika kalla. Domin wasu fina-finai. Misali Jamilu Jidda da Kishiyar gida da dakin Amarya, babu abin da ke cikin wadannan fina-finai, face koya wa mata yadda za su bijire wa mazajensu da tsananin gaba, da kin abokiyar zama (Kishiya. Hakan ya fito ne da umarnin Allah da Annabi (SAW). Kuma wasu matan na daukar dabi’un da suka gani a fim.
’Yan uwa matan wa zai aure su idan muka ki kishiya. Mu ma muna da ’ya’ya da kanne. Daga Mamman AbdulBasid Gombe 08125518587.

Sakonnin waya
Muna tare da Gwamna Amaechi

Editan Aminiya mai kwarjini ki tunatar da Gwamnan Jihar Bauchi in maye ya mance, uwar diya ba ta mance ba. Ka manta da cinaman da ka yi wa jam’iyyar ANPP, ka koma PDP an dai ji kunya. Muna tare da Gwamna Amaechi da Abdul Aziz Yari. Daga Malam Kabiru Hamdala Gusagu GRA 08066272283.

Ga Gwmanan Bauchi
Ko Jihar Bauchi ta yi sa’ar Gwamna kuwa? Sakona zuwa Gwamna Malam Isa Yuguda makarantunka ba koyarwa musamman Katagun ba ma samun isasshen karatu. Ga ba albashi to gaskiya Yuguda ka sauya hali, in ba haka ba, akwai 2015. Daga Faisa Muhammad Sani Gazas Chinade 07039566988.

Kira ga masoya
Assalam Aminiya don Allah a mika min gaisuwata ga masoya. Edita ina so ka isar min da shawarwari ga masoya, ya kamata musan bin da muke, domin akwaimu da yaudara. Su kuwa akwai jan aji, ya kamata mu san abin da muke. Daga Faisal M. Sani Gazas 07039566988.

Ga Nasir Babi
Allah Ya yi wa baban marubuci Nasir Babi jagora muna goyon bayanka dukanmu matasan Wudil. Daga ’Yan kungiyar Hadinkai da Taimakon Juna. 08032603070.

Ga Kawu Sumaila
Edita ka mika min gaisuwata ga Kawu Sumaila. Allah Ya yi mana jagora. Nagode. Daga M.D. Sani Bararo Kano Hausawa. 08038492252.

Zuwa ga Aminiya
Shin Katsinawa sun fi karanta Aminiya ne? Kuma sun fi turo sako mai ma’ana. Domin mu Kanawa muna da kishi. Daga Auwal Adam Shayaki T/Wada, Nasarawa Kano 08141144345.

Ta’aziyya Janar Kontagora
Edita ka isar min da sakon ta’aziyya ga iyalan Marigayi Janar Mamman Tsoho Kontagora da Maigirma Gwamna Jihar Neja, Dokta Mu’azu Babangida Aliyu da sauran ’yan Najeriya. Allah Ya jikansa. Amin. Daga Hussaini M. Zamfara FCT, Abuja 08060997984/08185711862.

Ga Hukumar ’yan sanda
Aminiya jaridar talakawa don Allah ina so ku isar mini da sakona ga hukumar ’yan sanda ta Jihar Kano da ta gaggauta bi wa ’yan uwan marigayiya Maryam Alasan , wadda makwasfciyarta, tare da ’yan uwanta suka kashe. Daga Surajo suleja IBB Market 07037780446.

Ga Janar Buhari
Salam Editan ina So ka bani dama domin in mika sakon gaisuwa ga Gen Muhammadu  Buhari Uban Talakawan Najeriya Kuma Wanda zai share musu hawaye 2015 In Allah Ya Yarda.Muna Tare Da Baba,ba Gudu ba Ja da  Baya. Sai Baba Buhari 2015 No Lied 9ja Guyd muna tare da Kai Baba. Daga Sultan Musa 08183145623.

Ta’aziyyar hadarin jirgin Dana
Inja mika ta’aziya ga iyalan wadanda hadarin jirgin saman Dana ya rutsa da su, yau shekara daya kenan.Allah Ya rahamshe su. Daga Sadi Musa Khalid Jos 07033306067.

Ga Nazifi Asnanic
Edita ka mika min gaisuwar bangirma ga mawakin nan Nazifi Asnanic. Daga 08066341524.

Aminiya ko Credit ake saya?
Nawa ake biya a turo sako, sakona na bakwai ke nan ba taba sawa ba. Ya kamata a yi adalci. A fad amana idan Credit ne ake saya to ya ake saya. Daga Habibulla Sunusi danja, Jihar Katsina 08092602127.

Dokar tabaci
Dokar tabaci ko dokar kashe mutane. Soja sun samu abin da suke so. Allah Ya kawo mana zaman lafiya. Daga Abdullahi KYD 08031835216.
Dokar hana bara

Dokar hana bara a Najeriya wani sabon salon zalunci ne kawai. Daga AbdulAziz A’Nu Maska Funtuwa 07068549745

Aminiya ta biya ni
Editan Aminiya ka jawo mini jama’a. Gaisuwa da jinjina ga ma’aikatanka. Kuna biyana da za mu yi murabus, amma mun dawo. Saboda kun fara fitar da sakona, har sau biyu. A kan haka na samu masoya a fadin Najeriya, maza da mata, har suna daukar lambata. Kanawa da Katsinawa da Zamfara sun kirani. Daga Bashir Adamu Moriki Zamfara 07036951482.

A kara matakan tsaro
Don Allah ku gaya wa shugaban kasar nan Goodluck ya ba da tsaro mai inganci ga al’ummar kasar nan ga baki daya. Daga Aliyu Musa Aljannare 08128091662.

Editan Aminiya matsoraci ne
Salam Editan Aminiya ban gane ba, kana tsoron Gwamnan Kano ne? Idan na aiko da sako ba ka rubutawa, ko kaima dan PDP ne? Daga Daimond Aliyu Harazimi 08144079362.

Ta’aziyata ga Sarkin Kano
Salam Edita don Allah ka isar min da sakon ta’aziyata ga Maimartaba Sarkin Kano, Dokta Alhaji Ado Bayero, bias rasuwar mai dakinsa, Hajiya Rabi, Umma Uwar Soro. Allah Ya jikanta, Ya gafarta mata; Ya bai wa ’ya’ya da ’yan uwa hakurin jure rashin. Daga Alhajin Dubai G/Bajaj 07038605362.

Ga jami’an tsaro
Don Allah ina son shiga fagen shirye-shiryenku. Kuma jami’an tsaro ku ji tsoron Allah, ku daina kashe talakan Najeriya da sunan Boko Haram; ba gaskiya a cikin kotuna za ku koma ga Allah; ba za ku dawwama a duniya ba. Ku gama kashewar ku je ku tarar da abin da kuka aikata. Daga aBdulbasiru Magaji Zangon Marke Bakori.