Shugaba Bola Tinubu ya tura tawaga ta musamman domin zuwa ta’aziyyar mutane fiye da 100 da suka mutu tare da wasu da dama da suka samu rauni a hatsarin tankar mai a Jihar Jigawa.
Tinubu, wanda shi da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima suke ƙasar waje, yau umarci ƙarƙashin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, su isar da tallafin gaggawa na kayan abinci da magunguna da kuma matsuguni ga mutanen da hatsarin ya shafa
Ya kuma umarce su da su ziyarci wurin da abin ya faru domin gane wa kanta, sannan su je dubiyar sama da mutane 50 da suka kone a hatsarin, da ke samun kulawa a asibiti.
Sanarwar da kakakinsa, Bayo Onanuga ya fitar ta ce tawagar Shugaban Kasa za ta ƙunshi Ministan Tsaro, Muhammad Bafaru Abubakar da Ministan Sufuri, Sanata Saidu Alkali; Shugaban Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Ƙasa (FRSC) Shehu Mohammed; da Hadimin Shugaban Ƙasa kan Tattauna da Jama’a (Arewa maso Yamm), Abdullahi Tanko Yakasai.
- Boko Haram ta fille kan mutum 4 a Borno
- HOTUNA: Yadda aka kama ɓarawo bayan ya fasa gida ya kwashe kayan ciki
Gwamnonin Arewa sun jajanta
Kazalika Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa sun jajanta wa Gwamna Umar Namadi bisa ibtila’in da ya faru sakamakon fashewar tankar man.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana takaicinsa bisa hatsarin da ya auku a Ƙaramar Hukumar Taura.
Ya jaddada muhimmancin haɗa kai da hukumomin bayar da agaji da kuma ɗaukar matakan kare aukuwar irin haka, musamman ma ta hanyar wayar da kan jama’a.
Inuwa Yahaya, wanda ya roƙa mamatan samun rahama da kuma waraka ga majinyatan cikinsu, ya kuma yi addu’ar Allah Ya ƙarfafi iyalansu, Ya ba su juriya game da wannan lamari.
Sanarwar da hadiminsa Ismail Uba Musulmi ya fitar ta jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin gwamnatocin jihohi a ɓangare bayar da agaji.