✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsarin mota ya lakume rayuka 13 a Neja

Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), ta tabbatar da rasuwar mutum 13 da wasu 14 da suka ji rauni a hatsarin mota da ya auku…

Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), ta tabbatar da rasuwar mutum 13 da wasu 14 da suka ji rauni a hatsarin mota da ya auku a kan titin Bida/Mokwa da ke Jihar Neja a ranar Talata.

Kwamandan Hukumar Reshen Jihar, Joel Dagwa, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Minna, babban birnin Jihar.

Dagwa, ya bayana cewa hatsarin ya faru da misalin karfe 6:30 na safiyar Talata a kauyen Panti, wanda ya rutsa da motar sintirin hukumar mai lambar ZUR690XA da lambar bus TN421XA.

“Kimanin mutane 27 ne hatsarin ya ritsa da su, 13 daga cikinsu sun rasu nan take, sauran 14 da suka jikkata kuma aka garzaya da su Cibiyar Lafiya ta Gwmnatin Tarayya da ke Bida, da Asibitin Kwararru na Kutigi don samun kulawar da ta kamata,” inji shi.

Kwamandan na FRSC yace ana zargi hatsarin ya auku ne sakamakon kwacewar motar.