✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsarin mota ya yi ajalin wata mata tare da raunata wasu

An tabbatar da rasuwar matar bayan an kai ta asibitin koyarwa na Jami’ar OAU da ke Ile-Ife

Wani hatsarin mota a ya yi sanadin mutuwar wata mata a kan babban titin Gbongan-Ibadan a Jihar Osun.

Hatsarin ya ritsa da wata mota ce kirar Toyota da kuma mota kirar Corolla.

Jami’an ’yan sanda da Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) sun kai agaji wajen tare ceto wasu daga cikin wanda hatsarin ya ritsa da su.

Yara uku da wani babban mutum guda daya sun samu raunuka kuma an garzaya da su zuwa asibiti.

Kakakin FRSC ta Jihar, Misis Agnes Ogungbemi, ta ce hatsarin ya auku ne sakamakon kwacewar mota kuma da an kimanta gudu ba za a samu salwantar rai ba.

Agnes Ogungbemi ta ce yara uku da karin mutum daya da suka ji rauni, motar agajin gaggawa ta ba su kulawa, sannan aka tafi da su asibiti.

Ta kara da cewa matar an dauke ta zuwa asibitin koyarwa na OAU da ke Ile-Ife, inda aka tabbatar da mutuwar ta.

Har wa yau, ta ce jakar hannu da katin cirar Kudi na ATM da kayan abinci da sauran abubuwan da aka samu a motar matar an damka su ga hannun ’yan sanda.