Akalla mutum tara ne suka mutu yayin wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su, yayin da wasu mutum 10 suka ji raunuka a kan titin Gaya zuwa Dutse da ke tsakanin Jihohin Kano da Jigawa.
Hatsarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin a kauyen Sabaru kusa da garin Gamoji a Karamar Hukumar Gaya a Jihar Kano, tsakanin motar kirar Toyota Hiace da kuma wata kirar Sharon.
- ‘Masu garkuwa da Kwamishinana za su fuskanci tsattsauran hukunci’
- Juyin mulki: Sojojin Burkina Faso sun tsare Shugaban Kasa
Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewar daya motar kirar Toyota ta fito ne daga garin Azare a Jihar Bauchi, yayin da Sharon din ke hanyarta ta zuwa Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
Aminiya ta gano an dauke gawar mutanen da suka rasu zuwa babban asibitin Gaya, inda ake kokarin tuntubar ’yan uwansu, yayin da kuma wanda suka ji rauni ake ba su agajin da suke bukata.
Mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) na Jihar Jigawa, Ibrahim Gambo, ya tabbatar da faruwar hatsarin.
Ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin motar bas kirar Hummer mai lamba DRZ 846 XA da kuma mota kirar Sharon mai lamba DAL 830 XA.
Gambo ya ce gudun wuce sa’a da kuma shiga hannun da ba na matuki ba ne ya haifar da hatsarin tsakanin motocin biyu, wanda suka yi gaba da gaba.
Hukumar ta sanar da cewar mutum 19 ne hatsarin ya rutsa da su, maza 17 da kuma mata biyu.
Dukkan mutum taran da suka mutu maza ne, sai kuma mata biyu da suka samu raunuka daban-daban.