✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 19 a Filato 

Rahotanni sun bayyana cewar fasinjojin motar baki ɗaya sun rasu.

Aƙalla mutane 19 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a yankin Hawan Kibo da ke ƙaramar hukumar Riyom a Jihar Filato.

Hawan Kibo na da tazarar kimanin kilomita 60 daga Jos, Babban Birnin jihar.

Kakakin Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Filato, Peter Yakubu, ya shaida wa Aminiya cewa duka fasinjojin da ke cikin motar sun mutu.

Ya ce, “Babu wanda ya tsira daga cikin fasinjojin. Mutum ɗaya kawai aka kai asibiti amma daga baya ya rasu.

“Mutum 18 sun rasu nan take a wajen hatsarin, yayin da guda ɗaya ya rasu a asibiti.”

Wani ma’aikaciya a Asibitin Ƙwararru na Riyom, ya shaida wa wakilinmu cewa an kai gawarwakin wasibitin da safiyar ranar Litinin.

“Duk mutanen da aka kawo mana sun riga sun rasu. Wasu gawarwaki sun yi muni sosai ta yadda ba a iya gane su.

“An kai gawarwakin ɗakin ajiyar gawa a Jos saboda matsalar wutar lantarki a ƙaramar hukumar Riyom,” in ji ta.

Ta kuma ce motar da ta yi hatsarin tana kan hanyarta daga Jihar Adamawa ne zuwa Abuja lokacin da lamarin ya auku.

Rahotanni sun bayyana yadda ynkin Hawan Kibo yake fama da yawan hatsari sakamakon rashin kyawun hanya.