Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), reshen Jihar Kwara ta tabbatar da mutuwar mutum 11 a hatsarin mota a ranar Lahadi.
Kwamandan hukumar a Jihar, Jonathan Owoade ne ya tabbatar wa manema labarai faruwar hatsarin a Ilorin, inda ya ce lamarin ya faru a kan titin Jebba zuwa Bode zuwa Saadu.
- ’Yan bindiga sun yi awon gaba da daliban jami’a 4 a Nasarawa
- Maraba da riga-kafin zazzabin cizon sauro
Owoade ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar Toyota Corolla mai lamba AAA250CB da kuma motar bas kirar Toyota Hiace mai lamba LAP 179 XA.
Ya ce hatsarin ya ritsa da mutum 26, inda 11 daga ciki suka rasu, yayin da mutum 15 kuma suka ji rauni.
“Da yammacin nan, mun sami kiran waya game da wani hatsari da ya faru da misalin karfe 4:00 a kauyen Onipako, kusa da hanyar Bode zuwa Saadu titin Jebba.
“Tukin ganganci ne ya haddasa hatsarin, daga cikin mutum 26 da ke cikin ababen hawan, 15 sun ji rauni sannan mutum 11 suka rasa rayukansu.
“Ba ma fatan sake samun irin wannan hatsarin, muna kira ga masu ababen hawa musamman na haya da rika yin hakuri yayin tuki.
“Mutum rai daya gare shi, daga shi babu wani,” a cewarsa.
Kwamandan ya kuma ce an mika wadanda suka ji rauni zuwa asibitin Emmanuel da ke Jebba don ba su kulawa, wanda suka rasu kuma an ajiye gawarwakinsu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin.