✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 10 a hanyar Jos zuwa Bauchi

Wata tirela ce ta kwace wa direbanta, ta daki wasu motocin

Akalla mutum 10 ne suka rasu, 15 kuma suka jikkata sakamakon wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Jos zuwa Bauchi.

Wani da lamarin ya faru kan idonsa ya shaida mana cewa da misalin karfe 8:00 na safe ne wata tirela makare da kaya da ke kan hanyarta ta zuwa Bauchi ta kwacewa direbanta, sannan ta ture motoci da dama.

Ya kuma ce sakamakon haka, mutum 10 sun mutu nan take, lamarin da ya haifar da cinkoson ababen hawa a hanyar.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), Alphonso Godwin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kuma ce wani karfen juya motar ne ya lalace sannan ya sa motar ta ki sarrafuwa.

“Mutum 10 sun rasu, sai 15 kuma da suka samu munanan raunuka sanadiyar hatsarin,” inji Kwamandan.

Ya kuma ce wadanda suka ji raunin na kwance a asibitin Toro da ke jihar Bauchi, yayin da gawarwakin kuma aka kai su dakin adana gawarwaki na asibitin Jami’ar Bingham da ke Jos.