Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Ilesa zuwa Akure, ya salwantar da rayukan fiye da mutum 20 a ranar Litinin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, SP Yemisa Opalolo da ta Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC), Agness Ogunbgemi, sun tabbatar wa da Aminiya lamarin.
- Hatsarin mota ya lakume rayuka 7 a Binuwai
- Hatsarin tireloli ya salwantar da rayukan mutum 10 a Adamawa
Tuni dai jami’an ‘yan sanda da na Hukumar FRSC sun kai dauki inda suka yi gaggawar garzaya wa da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin RTC da ke Ipetu-Ijesa tare da killace mutanen da suka mutu a Asibitin Wesley da ke Ilesa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ta ce hatsarin ya auku ne sakamakon wata babbar motar dankon makamashin gas da ta kwace daga karkashin gudanawarwar matukinta a yankin Igbelajewa na jihar Osun, inda takwararta ta Hukumar FRSC ta ce ba a iya tantance adadin mutanen da hatsarin ya rutsa da su ba.
Mashaida wannan mugun gani sun tabbatar da cewa mutum fiye da ashirin sun riga mu gidan gaskiya a hatsarin ciki har da wadanda suka kone kurmus ta yadda ba a iya gano ko su waye.