✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsarin mota ya ritsa da Shugaban Ukraine

sai dai na ce shugaban bai ji wani mummunan rauni ba

Hatsarin mota ya ritsa da Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky.

Kakakin Shugaban, Sergiy Nikiforov, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook da sanyin safiyar Alhamis.

Sai dai ya ce Shugaban Zelesky bai ji wani mummunan rauni ba a hatsarin.

Ya ce, “Wata motar fasinja a birnin Kyiv ta yi taho-mu-gama da motar Shugaban Kasa da wata ta daya daga cikin masu rakiyarsa.

“Ma’aikatan lafiyar da ke cikin ayarin na Shugaban Kasa sun ba fasinjan taimakon gaggawa, sannan suka mayar da shi cikin motar daukar marasa lafiya.

“Shi kuma Shugaban Kasa ya sami kulawa daga likita, kuma babu wani mummunan rauni a jikinsa. Jami’an tsaro za su gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin hatsarin,” inji Kakakin Shugaban.

Sai dai a wani bidiyo da ya wallafa jim kadan da faruwar lamarin, Shugaba Zelensky ya ce bai jima da dawowa daga wani yanki ba da ke kusa da birnin Kharkiv.

Hatsarin ya faru ne bayan Zelensky ya ziyarci birnin Izyum da ba a jima da kwato shi ba daga dakarun Rasha ranar Laraba, wanda birni ne mai matukar muhimmanci a Arewa maso Gabashin kasar.

%d bloggers like this: