Mutum 13 sun mutu sakamakon hatsarin mota a kan babban titi Ilori-Jebba-Mokwa da ke Karamar Hukumar Moro ta Jihar Kwara.
Shaidu sun ce wata motar bas mai cin 18 da ke hanyarta ta zuwa Sakkwato ce ta yi karo da wata tirela da ke tsaye. Daga baya wata bas mai ci mutum 18 da ta taso daga Arewa zuwa Legas ta kwace.
- ’Yan bindiga sun harbe wani mutum har lahira
- Za a bude makarantu ranar Litinin a Taraba
- Zaben Edo: Za a rufe hanya karfe 12 ranar Juma’a
“Nan take mutum 11 suka rasu a hatsin farkon sannan wasu biyu suka rasu a na biyun. Iyalan daya daga cikin mamatan sun tafi da gawarsa”, inji Kwamandan Hukumar Kare Aukuwar Hadurra ta Kasa (FRSC) a Jihar Kwara, Gbenga Owoade.
Ya ce mutum takwas da suka tsallake rijiya da baya a hatsarin na ranar Alhamis, na samun kulawa a wani asabibiti da ke garin Bode Saadu a Karamar Hukumar.
Wakilimun ya ce an garzaya da gawarwakin mamatan zuwa dakin ajiyar gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilori (UITH).
Kwamandan na FRSC a Jihar ya kuma dora alhalin aukuwar hatsarin a kan rashin kulawar direbobin.
“Ya kamata kowa ya fahimci ce idan aka mutu ba a dawowa”, kamar yadda ya yi bayani.
Alkaluma sun suna mutum 136 ne suka mutu sakamakon hatsari a kan hanyar ta Ilorin-Jebba-Mokwa daga watan Janairu zuwa Satumban 2020 inda mutum 535 suka samu raunuka.
Yawan hatsari da aka samu a kan babbar hanyar a tsawon lokacin ya kai 1,187.