Hukumar Kiyaye Hadura ta kasa (FRCS) ta tabbatar da rasuwar mutum 21 cikinsu har da dalibai, a wani hatsarin mota da ya auku a yankin Mgbowo da ke Karamar Hukumar Awgu ta jihar Enugu.
Kwamandan FRSC na jihar, Ogbonna Kalu, ya shaidawa jaridar Punch ta wayar tarho, cewar lamarin ya faru ne a ranar Laraba.
- Mutum 22 sun kone a hadarin mota
- Uwa ta kashe jaririnta a Enugu- ’Yan sanda
- ‘Yadda muka rasa ’yan uwanmu 24 a hadarin mota’
- Hadarin mota ya kashe mutum 9 a Enugu
“An rasa rayuka 21 ciki har da wasu dalibai da motar makaranta ke dauke da fiye da dalibai 50.
“Amma daga cikin wanda suka mutu, akwai masu tafiya a gefen hanya”, cewar Kalu.
Ya bayyana cewa bayan bincike sun gano cewar tukin ganganci ne ya haifar da hatsarin inda wata tirela a kan babban titin Awgu ta kwace kuma murkushe motar makarantar da ke dauke da dalibai sama da 50 a cikinta.
Bayan tabbatar da rasuwar mutane 21 an samu wanda suka ji rauni da dama.
Wani ganau ya ce direban motar ya tsere cikin daji ganin irin ta’asar da ya tafka.