Akalla mutum bakwai sun rasu a garin Kwanar Dangora da ke Karamar Hukumar Kiru a Jihar Kano sakamakon wani hatsarin mota bayan dawowa daga taron kamfen din dan takarara Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a Kano.
Hatsarin ya auku ne ranar Laraba a kan babbar hanyar Kano zuwa Zariya, kamar yadda shaidun gani da ido suka tabbatar wa Aminiya.
- Za a binciki yadda hannun jariri ya rube a asibitin AKTH da ke Kano
- A karshen watan Yuni za mu daina biyan tallafin man fetur —Ministar Kudi
Shaidun sun ce hatsarin ya faru ne wajen misalin karfe 7:00 na dare, yayin da motar ta je ta daki wata tankar mai, inda nan take mutum bakwai daga cikin 10 da ke motar suka rasu, ragowar kuma suka ji raunuka.
Da yake zantawa da Aminiya, wani wanda yake cikin ayarin motocin da suka halarci kamfen din mai suna Tukur Lawan, ya ce mutum biyar ne suka rasu nan take, yayin da daga bisani kuma ragowar biyun suka rasu a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.
Ya ce, “Tare muka halarci taron, inda a kan hanyarmu ta dawowa, wannan abin bakin cikin ya faru.
“Hatsarin ya auku ne lokacin da direban tankar man ya yi aron hannu a kan titin na Kano zuwa Kaduna. Bayan sun hadu ne sai tankin babbar motar ya tsinke ya kuma hada Golf din da da shingen titi,” inji Tukur Lawan.
Ya ce wadanda lamarin ya ritsa da su sun hada da Bala Kariya da Barau Kariya da Hamza Huntu da Danladi Gidan Algaita da Musbahu Gidan Diraman da Yakubu Gidan Diraman da kuma Lawan Gidan Diraman.
Shi ma wani mazaunin yankin, Mahmud Abubakar ya ce ilahirin yankin yanzu ya shiga cikin alhini, inda shugabanni da dama, ciki har da ’yan siyasa suka halarcio jana’izar mutanen da aka yi a kauyukansu daban-daban.
To sai dai da wakilinmu ya tuntubi Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta bakin kakakinta, Abdullahi A. Labaran, ya ce har yanzu ba su sami rahoton aukuwar hatsarin ba.