Akalla mutum 30 sun kone kurmus yayin da wasu fasinjoji 12 kuma suka sami raunuka a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a Tashar Musa da ke kan hanyar Zariya zuwa Kano a ranar Alhamis.
Da yake tabbatar da aukuwar hatsarin, Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) shiyyar Zariya, Abdulhamid Yakasai, ya ce motoci guda uku; kirar Homa guda biyu da Golf guda daya hatsarin ya shafa.
- Kisan Hausawa a fadan kabilanci ya janyo zanga-zanga a Sudan
- Kowanne dan Najeriya yanzu yana da hannun jari a NNPC – Mele Kyari
Ya alakanta hatsarin da gudun wuce kima da kuma kokarin wuce na gaba ba tare da la’akari a da wasu direbobi ke yi ba a lokacin da suke tuki.
Yakasai ya kuma ce suna kokarin gano daga inda motocin suka taso da kuma lambobinsu domin sanar da ‘yan uwansu.
Tuni dai aka kai wadanda suka sami raunuka Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya tare da gawarwakin guda 30.