✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Hatsarin kwale-kwale ya kashe ’yan Najeriya sama da 400 a wata 16’

Ana alakanta lodin da ya wuce kima da cewa shi ke haddasa hatsarin.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa hatsarin kwale-kwale ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan Najeriya sama da 400 a cikin wata 16 kacal.

Mamba a Majalisar Wakilai, Hon. Hamisu Ibrahim ne ya bayyana hakan, yayin da yake gabatar da wani kudirin a zauren Majalisar ranar Talata.

A cewarsa, an sami rahotannin mutuwar sama da mutum 300 a hatsarin a sassa daban-daban na Najeriya a shekarar 2020, yayin da sama da 100 kuma suka mutu tsakanin watannin Mayu da Satumban 2021.

Dan majalisar ya ce galibi dalilan da suke haddasa kifewar sun hada da lafta wa jiragen nauyin da ya wuce kima, rashin kula da su, gudun wuce sa’a, tukin ganganci da kuma rashin yanayi mai kyau.

“Yawan kifewar jiragen ruwa da ake samu a kasar nan na faruwa ne sakamakon kin bin dokokin sufuri na ruwa, musamman ta hanyar lafta musu mutane fiye da ka’ida, a yunkurinsu na samun kudi mai yawa,” inji Hon. Hamisu.