Akalla mutum biyar ne suka mutu yayin da wasu suka ji rauni sakamakon wani hatsarin da jirgin saman soji ya gamu da shi yayin sauka a Sudan ta Kudu.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata yayin da jirgin ke dauke da wasu dakarun sojin ma’aikatar tsaron Sudan.
- An rufe makarantu a Indiya saboda zanga-zanga kan hana sanya hijabi
- NAJERIYA A YAU: Laifin Wane ne Rashin Damawa Da Matasa A Mulkin Najeriya?
Rahotanni sun ce jirgin na dauke da wasu muhimman takardu da ya dauko daga garin Bentiu zuwa Rumbek.
Ministan Ilimin Kudancin Sudan Awut Deng Acuil, ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya ce takardun na da matukar muhimmanci.
A baya-bayan nan dai an fuskanci hatsarin jiragen sama a kai a kai a Sudan ta Kudu.
Ko a shekarar 2018, mutum 19 sun mutu sakamakon hatsarin da wani karamin jirgin daukar fasinja ya yi a kan hanyarsa ta zuwa Yirol daga Juba, babban birnin kasar.
Kazalika, a watan Maris din 2020, wani jirgi ya yi hatsari a Arewa maso Gabashin Jihar Jonglei, wanda hakan ya salwantar da rayukan mutum 19.
A watan Nuwambar 2021 ma an sake samun hatsarin wani jirgin saman, wanda mutum biyar suka ce ga garinku nan a yankin Maban da ke kasar.