Jirgin da ya kai kayan agajin yana dauke da kayayyaki 1,000 na kula da munanan raunuka da kuma wasu 1,000 na tiyata.
Wata takarda da WHO ta fitar ta ce, za ta raba kayayyakin agajin ga daukacin asibitocin da ke kasar ta Labanan wadanda suke karbar marasa lafiya daga Beirut, saboda asibitoci 3 ba sa aiki sakamakon hadarin sai 2 da suka lalace.
“Hakika an jarrabi mutanen Labanan da rugujewar muhimman wurare”, a cerwar Hukumar.
Idan ba a manta ba hatsarin da ya auku ranar Talata ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da rikicin siyasa, da matsalar tattalin arziki da kuma annobar coronavirus sai kuma matsalar ’yan gudun hijira daga kasar Siriya wadanda suka kai dubu 900,000.