✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsari ya ritsa da ayarin motocin Gwamnan Bauchi

Akalla jami’an ’yan sanda 10 ne suka jikkata a wani hatsari da ya ritsa da ayarin motocin Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad a ranar Litinin.…

Akalla jami’an ’yan sanda 10 ne suka jikkata a wani hatsari da ya ritsa da ayarin motocin Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad a ranar Litinin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, hatsarin ya auku ne a yayin da gwamnan ya kai ziyarar gani da ido kan aikin gina sabon titi mai tsayin kilomita 60 a Karamar Hukumar Tafawa Balewa.

Ana gina sabon titin ne domin game hanyar mazauna Karamar Hukumar Tafawa Balewa zuwa Yelwan Duguri da kuma kewayen Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya auku ne a yayin da wata mota kirar Toyota Hilux dauke da jami’an ’yan sandan ta sauka daga hanya inda ta yi allankafura har sau biyu, lamarin da ya tirnike hanyar da kura ta yadda dole al’umma suka rintse gannansu.

Sai dai an yi sa’ar gaske babu rai ko daya da ya salwanta a yayin da aka garzaya da jami’an ’yan sandan da lamarin ya shafa zuwa Babban Asibitin Bununu da ke Karamar Hukumar Tafawa Balewa domin ba su kulawa.