✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsaniya Ta Barke A Majalisar Dattawa Kan Kuɗin Rabon Tallafi

Sanatoci na zargin an yi rashin adalci a rabon kuɗin da aka ba su domin al’ummar mazabarsu.

Majalisar Dattawa ta faɗa cikin ruɗani a zamanta na wannan Talatar sakamakon gano yadda aka miƙa kudin tallafin Gwamnatin Tarayya ga Sanatoci domin raba wa jama’a a mazabarsu.

Tun da farko dai ɗauko muhawara ne kan zargin da Sanata Abdul Ningi, shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa, ya yi a wata hira da BBC Hausa.

Sanata Ningi ya yi ikirarin cewa an yi mummunan rufa-rufa a Kasafin kudin shekarar 2024 har na makudan kudade Naira Tiriliyan Uku da da miliyan dari bakwai.

Bankaɗar da Sanata Ningi ya yi ce ta janyo barkewar hatsaniya a tsakanin Sanatocin.

Zaman majalisar ya nemi ya gagara a lokacin da Sanata Jarigbe Jarigbe ya bayyana cewa an bai wa wasu Sanatoci Naira miliyan 500 a matsayin abin da za su taimaka wa mazabarsu yayin da wasu kuma suka samu Naira miliyan 200.

Wannan tonon silili dai bai yi wa wasu Sanatoci daɗi ba, inda majalisar ta ruɗe da ihu, wanda da ƙyar Shugaban Majalisar Godswill Akpabio ya dawo da zauren Majalisar cikin hayyacinsa.