Akalla matafiya 19 ne suka rasu a hanyar Kaduna zuwa Abuja a daren ranar Lahadi, sakamakon hatsari da ya ritsa da su a daidai garin Kateri.
Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 8 na dare, kuma nan take mutum 16 suka rasu, uku kuma suka rasu a asibiti daga baya.
- Mai jego da jaririyarta sun tare ofishin gwamna kan rashin biyan albashi
- Mahara sun bindige mutum 40 a Nijar
- ‘Kashe $1.5bn wajen gyara matatar man Fatakwal almubazzaranci ne’
- ’Yan taratsi sun umarci kamfanonin mai su fice daga Akwa Ibom
Hatsarin ya auku ne da wata babbar mota kirar DAF, wadda ta taso daga Legas zuwa Kano, dauke da fasinja 53.
Da yake tabbatar da faruwar hadarin, Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura FRSC reshen Jihar Kaduna, Hafiz Mohammed, ya sce mutum 19 sun mutu, yayin da 34 suka ji rauni daga cikin mutum 53 da ke cikin motar.
Ya kara da cewa an ajiye gawarwakin a dakin ajiye gawa na Babban Asibitin garin Doka da ke kan hanyar Kaduna-Abuja.
Sannan ya ce ’yan uwan wanda suka rasun, tuni suka fara zuwa daukar gawarwakin ’yan uwan nasu, wanda yawancin daga Zariya da Kano suka fito.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ya ziyarci inda hadarin ya auku, inda ya ce gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya nuna alhininsa game da wanda suka rasa rayukansu, tare da addu’ar kiyaye faruwar hakan.
Ya kuma yi ta’aziyyar ga iyalan wanda hadarin ya ritsa da su sannan ya ja hankalin direbobi da su kasance masu kiyaye ka’idojin tuki.