✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hassan Sheikh Mohamud ya sake zama shugaban Somaliya

Shugaba Farmajo ya amince da shan kaye.

Tsohon shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a karshen mako.

Sheikh Mohamud ya lashe zaben ne da gagarumin rinjaye a gaban abokin karawarsa Mohamed Abdullahi Mohamed Farmajo.

Da kuri’u 165 ne dai sabuwar Majalisar Dokokin Kasar ta sahale wa Hassan Sheikh Mohamud zama sabon shugaban Somaliya.

Nasarar Mohamud na zuwa ne bayan da aka tafi zagaye na biyu tsakanin ‘yan takarar hudu ciki har da shugaba Farmajo da wa’adin mulkinsa ya zo karshe a watan Fabrairun bara.

A baya dai Mohamud ya rike mukamin shugaban kasa daga watan Satumban 2012 zuwa Fabrairun 2017, kuma a yanzu shi ne na farko da aka zaba sau biyu a matsayin shugaban Somaliya.

Tuni shugaba Farmajo ya amince da shan kaye, inda ya taya sabon shugaban murna tare da tabbatar masa da goyon baya.

‘Yan majalisun dokokin Somaliya ne suka gudanar da zaben sabon shugaban kasa a cikin matakan tsaro, wadanda adadin ‘yan majalisu 329 ne suka cancani kada kuri’a don tabbatar sabuwar gwamnati.

‘Yan siyasa 36 ne suka nemi takarar kujerar shuzagban kasa, ciki har da Shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed mai ci a yanzu.

Cikin ‘yan takarar har da tsoffin shugabannin kasar guda biyu da kuma mace daya tilo da ke zama tsohuwar Ministar Harkokin Wajen Kasar, sai da ‘yan takara biyu sun janye aniyarsu gabannin ranar zaben.

Manyan kalubale da ke jiran Hassan Sheikh Mohamud sun hada da dakile kungiyoyin ta’adda da tabbatar da hadin kan ‘yan kasar da yaki da cin hanci da rashawa da kuma samar da yyuka musamman tsakanin matasa.

Duk da cewa kasar Somaliya ta fara shiga yakin basasa tun 1991, kasar na gudanar da zaben shugaban kasar duk bayan shekaru hudu tun a 2000, kodayake na baya-bayan nan an jinkirta shi tun 2021.

A cikin watan Fabrairu Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF ya yi gargadin hana kudin tallafi kusan dala miliyan 400 har sai an yi zaben ‘yan majalisa da na shugaban kasa wanda aka kammala a tsakiyar watan Mayun 2022.

Somaliya ta jima tana fama da matsalolin hare-haren ‘yan ta’addan Al-shabab da ke ikirarin jihadi, baya ga rikicin siyasa da na fari da suka yi kaka gida a wannan kasa da ke yankin kahon Afirka, lamarin da ke zame wa sabon shugaban wani kalubale.