Jamila Muhammad Kogi, wadda aka fi sani da Jamila Kogi a Masana’antar Kannywood jaruma ce kuma mawakiya da take jan zare yanzu a masana’antar. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana yadda ta fara fim da waka da yadda take yin waka da harsuna biyar da kuma burin da take da shi:
Mene ne takaitaccen tarihinki?
Sunana Jamila Muhammad Kogi wacce aka fi sani da Jamila Kogi. Ni ’yar Jihar Kogi ce, na yi karatun firamare a Jihar Kogi, na yi sakandare a Jihar Neja, sannan na yi karatu a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) da ke Zariya, sannan ina da burin ci gaba da karatun nan ba da dadewa ba insha Allah.
Yaya aka yi kika fara waka?
Na fara waka ce sanadiyar karatun da na je a Zariya. A lokacin da na fara karatu sai na ji ina sha’awar in yi waka, to sai na yi wa wani ubangidana mai suna DJ Nuhu Barde magana na nuna cewa ina so in fara waka. Sai ya ce in je da Ahmad Alancy sutudiyo a gwada muryata. Da na je aka gwada muryata sai suka ji muryata kamar da ma na saba waka. A nan take sai muka yi waka maimakon gwaji, wannan ita ce waka ta farko mai sunan A je Makaranta. Daga nan ne na fara waka kuma ba ta ba ni wahala ba domin ni mace ce da duk abin da nake so nakan yi kokarin mayar da hankali har sai na iya. Don haka tun wannan lokacin nake ta samun daukaka har zuwa yau.
Me ya ja hankalinki kika yi sha’awar waka?
Abin da ya ja hankalina na fara waka shi ne in fadakar da al’umma kuma in samar wa kaina sana’a. Domin sana’a tana da muhimmanci a rayuwar dan Adam musamman a matsayina na ’ya mace.
Su wane ne iyayen gidanki a waka?
Suna da yawa domin duk wanda ya girme ni a fagen waka na dauke shi uban gidana, amma daga cikinsu akwai Nazir M. Ahmad, Ashiru Nagoma, Dan Auta, Umar M. Shareef, Oga Yarima, Alan Waka, Ahmad Alancy da sauransu.
A mata kuma akwai Zuwaira Isma’il da Fantimotin Waka da Zubaida Mu’azu da Fati Khalil da sauransu.
Sannan ina burin yin hadaka da Hadiza Bello wadda aka fi sani da Di’ja saboda mace ce mai kokari da jajircewa. Ina son in ga mata masu jajircewa.
Waka kawai kike yi ko kina hadawa da fim?
A da ina hadawa da fim, fim dina na fito na karshe shi ne Indon Kauye wanda na fito a matsayin ma’aikaciyar lafiya. Amma yanzu gaskiya ayyukana wato waka suna min yawa, inda har ba na cika samun lokaci wanda hakan ya sa ban cika shiga fim ba.
Kwanakin baya kin saki wakoki da Harshen Nufanci, yaya aka yi?
Ai ba wakokin Hausa kadai nake yi ba, ina wakokin da harshenmu na Egbira Koto, ina yi da Kakanda wato harshen mahaifiyata ina yi da Nufanci. Amma dai na fi yin waka da Hausa. Shi ya sa idan aka shiga shafina na YouTube wato jameela Kogi official za ka ga bidiyoyin da na yi na waka ba na Hausa ba ne kawai. Har da na sauran harsunan.
Ko kina yin waka da Ingilishi?
Eh ina yin waka da Ingilishi, ta karshen da na yi ita ce mai suna Come Around. Kuma ina son wakokin Ingilishin su ma. Ina da burin nan gaba in ci gaba da wakoki da Ingilishi. Wannan ya sa na zama daban, domin zai yi wuya a samu wadda za ta iya yin waka da harsuna biyar kuma ta isar da sakon da take bukatar isarwa.
Wadanne wakoki kika fi yi?
Ina wakoki da dama kamar wakokin siyasa da aure da wakar bikin murnar ranar haihuwa da bikin aure da wakar talla kamar tallata haja ko kamfani da wakar yabo da soyayya da sauransu.
Kina da albam da kika saki ne?
Ina da albam, amma ban sake shi a kasuwa ba. Amma ina shirin sakin albam, amma yanzu duk wakokin da na yi suna cikin shafina na YouTube mai suna jameela Kogi official kuma a duba shafina a Instagram mai suna official_jameela_kogi.
Sanan ba na mayar da waka siyasa, duk wanda ya biya ni zan masa waka domin ita ce sana’ata babu ruwana da gaba ko fada da kake yi da wani, ni na dauki waka sana’a. Kamar mai shago ne da ke sayar da shinkafa, sai wani ya zo saya kuma yana da ita, ka ga ai ba zai tura mai sayen shagon wani ba. Shi ya sa na zama ta kowa domin ba kudin wata ake biyana ba, waka sana’a ce kuma duk mai neman ci gaba ba ruwansa da fada ko gaba. Ya kamata mawaki ya zama na kowa ne.
Me za ki ce game da mawaka mata a Arewacin Najeriya?
Gaskiya mawaka mata sun yi karanci a Arewa domin matanmu suna ganin ba za su iya ba.Akasari sun fi yin amshin waka. Wato su kullum sun fi yi wa maza amshi wadansu ma ba su da wakokin kansu, wanda kuma haka bai kamata ba. In dai har maza za su yi suna a waka, su yi waka da kansu, a ganina mata ma za su iya kwatantawa. Don haka ya kamata mu dage kada mu rika bari ana barinmu a baya kuma mu rika girmama mawaka maza domin su ne sama da mu.
Ko kina da kira zuwa ga masoyanki?
Zan fara da godiya bisa soyayyarsu a gare ni. Lallai masoyana a ko’ina suke ina alfahari da su, kuma ina kira gare su da su ci gaba da nuna min soyayya da addu’a gare ni, kuma da yardar Allah ba zan ba su kunya ba.
Kina da wani sako ga abokan sana’arki mawaka?
Ina kira mu zama masu hakuri da juriya, mu kuma zama masu koyi da Manzon Allah (SAW) a duk inda muke. Mu rike Allah mu kuma ji tsoronSa, mu kuma dage da addu’a domin ita ce makamin mumini. Sannan mawaka mata da maza mu zama masu hakuri da junanmu tare da hada kanmu tamkar tsintsiya. Mu mata mu girmama na gaba da mu wato maza, su kuma maza su ji tausayinmu su tallafa mana a matsayinmu na mata da tunaninmu da hankalinmu bai kai nasu ba. Idan mun yi ba daidai ba su tsawatar mana domin su iyaye ne a wajenmu.
Kin yi wa Ali Nuhu, har kin saki bidiyon wakar, ko akwai wata alaka ce tsakaninku?
Alakata da Ali Nuhu ita ce mutunci da girmama juna. Shi uba ne a gare ni a Masana’antar Kanywood domin ya san mutuncin kanana kuma yana taimakonsu. Don haka babu abin da zan ce masa sai dai in ce Allah Ya saka masa da alheri da kuma gidan Aljanna domin ya gama min komai a wannan harka. Gaskiya ina matukar girmama shi, kuma ina kokarin girmama sauran ’yan Kannywood musamman na gaba da ni, kuma ina zaman lafiya da tsararrakina.
Me za ki ce game da yawan rikice-rikice da ake yi a Masana’antar Kanyywood?
Abin da zan fada shi ne Allah Ya kawo karshen rikice-rikicen da ake a Kanywood. Amma ina kira ga manyanmu musamman shugaban ni su yi gyara sosai domin akwai wadansu marasa tarbiyya da rashin sanin darajar manya a cikin Kanywood wadanda suke ja mana zagi a wajen jama’ar gari. Ba su girmama na gaba da su, gani suke yi su ma sun yi kudi kuma mene ne na gaba da su za su nuna musu, wanda hakan bai dace ba. Babba babba ne dole mu girmama shi, su kuma manyan ina kira gare su su rike girmansu kada su yarda wani abu ya kawo raini a tsakaninsu da ’yan bayansu.
Amma gaskiya abin takaici ne a ce muna fadace-fadace a tsakaninmu inda ake neman arziki. Ai ba a fada a wajen nema. Don haka mu yi hakuri da junanmu kamar yadda Hausawa ke cewa rayuwa zo mu zauna zo mu saba ne, dole sai an kai zuciya nesa kuma dole sai mun yi hakuri da juriya mu cire hassada da kyashi domin shi ne babban abin da ke kawo fadace-fadace tsakanimu. Don girman Allah don soyayyar da muke yi wa Manzon Allah (SAW) mu yi hakuri da junanmu. Idan ka bata wa wani ka ba shi hakuri komai ya wuce. Idan mun yi haka za mu kara samun nasara.