✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haske ya sauka a Jihar Osun —Atiku

Wannan nasara alama ce da ke nuna cewa Atiku na nan tafe.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce haske ya sauka a Jihar Osun bayan kammala zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar.

Cikin sakon taya Ademola Adeleke murnar lashe zaben da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya ce wannan nasara ta duk ’ya’yan jam’iyyar da kuma masu ruwa da tsaki da ita.

A cewar Atiku, “Haske ya sauka a Osun. Ina taya Sanata Ademola Adeleke murnar nasarar da aka samu.

Sakon da Atiku ya wallafa a shafinsa na Twitter
Hoton taya murna da Atiku ya wallafa a shafinsa na Twitter

“Har ila yau, ina taya jam’iyyar PDP murna da ’ya’yanta da duk masu ruwa da tsaki da suka taru don ganin wannan nasara ta tabbata.

Shi ma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya wallafa dogon sako a shafinsa na Facebook inda ya gode wa mutanen Jihar Osun bisa jajircewar da suka yi domin ganin sun zabi Adeleke.

Kazalika, Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya gode wa jama’ar Osun inda ya ce wannan nasara alama ce da ke nuna cewa Atiku na nan tafe.

Sakon da Tambuwal ya wallafa a shafinsa na Twitter
Hoton taya murna da gwamna Tambuwal ya wallafa a shafinsa na Twitter