✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar Bukola Saraki ta rasu

Mahaifiyar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ta riga mu gidan gaskiya

Allah Ya yi wa mahaifiyar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki, rasuwa.

Bukola Saraki, wanda shi ne tsohon Gwamnan Jihar Kwara, nada kansa ya sanar da rasuwar a ranar Talata.

Ya bayyana cewa nan gaba za a sanar da yadda za a gudanar da jana’iza mahaifiyar tasu mai suna Florence Morenike Saraki.

Ya sanar da cewa, “cikin alhini da mika komai ga Allah, muna sanar da rasuwar mahaifiyarmu, Florence Morenike Saraki, a yau (Talata) 18bga watan Yuni, 2024.

“Muna godiya da sakonninku na ta’aziyya kuma nan gaba za a sanar da shirye-shiryen jana’iza,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.