✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hasashe: Ronaldo da Messi na iya murza leda a kungiya daya

Ronaldo da Messi na iya murza leda a PSG a 2022.

Rahotanni daga birnin Paris na nuni da cewa akwai yiwuwar Paris Saint-Germain ta sayi Cristiano Ronaldo don hada shi da Lionel Messi saboda kungiyar na iya rasa Kylian Mbappe zuwa Real Madrid.

Rashin tabbas game da makomar Kylian Mbappe na iya sa PSG shiga neman Ronaldo, inji jaridar AS Dario da ke kasar Spain.

Yanzu haka Real Madrid na kan zawarcin Mbappe, wanda hakan ya sa PSG ta fara tunanin hada Messi da Ronaldo a kungiya guda, abin da masu fashin baki kan harkar wasanni suka yi ammanar cewa babu shakka  zai dauki hankalin masu ruwa da tsaki a duniyar kwallon kafa.

Jaridar AS dai ta rawaito cewa PSG ta zabi rabuwa da Mbappe kyauta ba tare da karbar kudin kowace kungiya ba a shekarar 2022 a maimakon saida wa Real Madrid a yanzu, yayin da kuma take fatar Ronaldo, wanda shi ma yarjejeniyarsa da Juventus za ta kare a 2022, ya maye gurbinsa.

Tuni dai tattaunawar sabunta yarjejeniya tsakanin Mbappe da kungiyar PSG ta tsaya cak bayan da ya yi watsi da tayin tsawaita zaman nasa da kungiyar.

Tun bayan daukar Messi da PSG ta yi hankalin mutane da dama ya koma kan kungiyar, domin ganin irin rawar da za ta taka a kakar wasanni.