Harry Kane ya karya tarihin Wayne Rooney na zama kan gaba a yawan ci wa Ingila kwallaye bayan ya ci ta 54 yayin da Ingila ta ci Italiya 2-1 a wasan shiga Euro 2024.
Kane, mai shekara 29 ya yi kan-kan-kan da Wayne Rooney mai rike da tarihin a gasar kofin duniya a Qatar, bayan da ya ci Faransa a wasan da aka fitar da su a kwata-final.
- Tarihi 5 da Ronaldo ya kafa a wasan Portugal da Liechtensen
- NAJERIYA A YAU: Ana Azumin Bana Cikin Mawuyacin Hali
Ya kuma ci kwallon ranar Alhamis a bugun fenariti a karawar hamayya da suka yi a Naples, filin wasa na Diego Maradona.
Kenan Kane ya zama kan gaba a yawan cin kwallaye a tawagar Ingila da kuma Tottenham.
Ya kuma ci wa Ingila kwallo 54 a karawa 81 da ya yi wa tawagar.
Declan Rice ne ya fara ci wa Ingila kwallo a minti na 13 da fara wasa, yayin da Italiya ta farke ta hannun Mateo Retegui, bayan da suka koma zagaye na biyu.
Ingila ta karasa wasan da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Luke Shaw jan kati, saura minti 10 a tashi daga wasan na hamayya.
Ga jerin ’yan wasan Ingila da suka ci mata kwallo sama da 40:
Harry Kane (Daga 2015): Ya ci kwallo 54 a wasa 81
Wayne Rooney (2003-2018): Ya ci kwallo 53 a wasa 120
Bobby Charlton (1958-1970): Ya ci kwallo 49 a wasa 106
Gary Lineker (1984-1992): Ya ci kwallo 48 a wasa 80
Jimmy Greaves (1959-1967): Ya ci kwallo 44 a wasa 57
Michael Owen (1998-2008): Ya ci kwallo 40 a wasa 89
Cikin kwallayen da Kane ya ci har da shida da ya zura a raga a Gasar Kofin Duniya a Rasha, wanda ya zama na uku dan kasar da ya lashe takalmin zinare a babbar gasar tamaula a duniya.
Na farko mai bajintar shi ne Garry Lineker a gasar kofin duniya a 1986 da kuma Alan Shearer a gasar nahiyar Turai a 1996
Ya kuma kafa tarihi da yawa a tawagar Ingila, wanda ya ci 16 a farkon shekarar 2021 zuwa karshenta.
Kane yana da jan aiki a gabansa idan yana fatan kalubalantar Cristiano Ronaldo mai kwallo 120 a yawan zura wa tawaga a tarihi.
Kwallo 204 da ya zura a raga a Tottenham ya zama na uku a jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Firimiyar Ingila.