Hukumomi a kasar Burkina Faso sun sanar da rasuwar mutum 120 a ranar Juma’a a wani hari da ’yan ta’adda suka kai yankin Arbinda da ke kan iyakar kasar.
Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar a daren ranar Alhamis ya bayyana cewa fararen 65 da ’yan ta’adda 58 sun mutu a sanadiyyar harin.
Hukumar ’yan sandan kasar ta sanar a kafar Facebook cewa ta yi nasarar fatattakar ’yan ta’adda da yawansu ya kai 400 a wani artabu da suka yi a ranar Alhamis.
Kazalika, jami’an tsaro sun ce sun samu nasarar kwace tarin bindigogi da harsasai a wurin da aka kai harin.
Hare-hare daga kungoyin ’yan ta’adda na ci gaba da kamari a kasashen da Yammacin Afirka.
Wasu daga cikin kungiyoyin tayar da kayar bayan ana zargin suna da alaka da kungiyar Al-Qaeda.
Duk da kokarin da jami’an tsaro ke yi a kasar na kawo karshen ta’adanci tun a 2015, kasar na ci gaba da fuskantar hare-hare.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan 1.2 ne suka tsere daga muhallansu don guje wa tashin hankali a hannun kungiyoyin ’yan ta’adda.