Gwamnatin Tarayya ta nemi mutane da kada su yi wata fargaba duk da gargadin da wasu kasashen yamma suka yi wa mutanensu masu shigowa Najeriya kan yiwuwar kai hare-haren ta’adanci.
Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed shi ne ya yi furucin a sanarwa da ya sanya wa hannu a jiya inda ya bayar da tabbacin daukar matakan da suka dace don kare lafiya da dukiyoyin ’yan Najeriya da baki.