✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin sojojin sama ya hallaka shugaban ISWAP, Sani Shuwaram, a Borno

Ana harsashen an kashe shi ne tare da wasu mayakan kungiyar

Akwai yiwuwar wani harin sojojin saman Najeriya a garin Marte na Jihar Borno, ya hallaka shugaban kungiyar ISWAP, Sani Shuwaram, bayan wasu hare-hare ta sama.

Kafar yada labarai ta PRNigeria ta rawaito cewa jiragen yakin rundunar samfurin, Super Tucano, sun yi ruwan wuta a wurare da dama a yankin, kuma ana kyautata zaton ya ritsa da sansanin da shugaban yake.

Bayanai dai na nuni da cewa Shuwaram ya mutu ne sanadiyyar raunukan da ya samu lokacin da hare-haren sojojin suka mamaye sansanin da ke Sabon Tumbuns a kusa da yankin Tafkin Chadi.

Kazalika, wata majiyar a sashen leken asiri na rundunar da ke yaki da ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas ta tabbatar da labarin ga majiyar tamu.

Majiyar ta kuma ce, “Sani Shuwaram na daya daga cikin ’yan ta’addan da aka raunata sakamakon hare-haren sojojin sama a Sabon Tumbuns da ke kusa da Kirta Wulgo a watan Fabrairun 2022.

“Jerin hare-haren da aka kai sun yi sanadiyyar kisan nashi tare da wasu mayakan kungiyar a wajen da suke samun kulawa, cikinsu har da Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi,” inji majiyar.

A wani labarin kuma, tuni kungiyar ta ISWAP ta maye gurbin marigayin da Malam Bako Gorgore, a matsayin sabon shugaban da zai maye gurbin Sani Shuwaram din.

Sai dai da aka tuntubi Kakakin Rundunar Sojojin Saman, Air Commodore Edward Gabkwet, ya ki cewa uffan game da kisan.

Amma ya tabbatar da cewa jiragen rundunar tare da tallafin sojojin kasa, sun kai munanan hare-hare a yankin da ake magana a kai.