Gwamnan Jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya tsawaita wa’adin zaman makoki a jihar zuwa ranar Larabar don ci gaba da nuna alhini game da rayukan da aka rasa a mummunan harin Owo.
Bayanin tsawaita wa’adin na kunshe ne cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai ga Gwamnan, Mista Richard Olatunde, wadda ya fitar a Akure.
Olatunde ya ce an tsawaita wa’adin ne saboda bukatar hakan da gwamnonin Kudu maso Yamma suka nuna na a ware kwana uku don su hadu su yi zaman makokin, wanda ya soma daga ranar Litinin zuwa Laraba a tsakanin jihohin Kudu maso Yamma.
Sanarwar ta ce, “Gwamna Akeredolu ya sake ba da umarnin a sassauto tutoci kasa-kasa a fadin jihar na tsawon kwanaki ukun da aka kara na makokin.
Idan dai ba a manta ba, Gwamna Akeredolu ya ba ba da umarnin sassauto tutoci kasa-kasa a fadin jihar na tsawon kwana bakwai, daga Litinin ta makon jiya zuwa Lahadin da ta gabata don nuna alhini da martaba rayukan wadanda suka mutu a harin.
“Gwamna Akeredolu ya nuna godiyarsa dangane da kauna da hadin kan da takwarorin nasa suka nuna masa tun bayan mummunan harin da aka kai a Owo,” inji Olatunde.
Aminiya ruwaito cewa gwamnan ya soke bikin Ranar Dimokuradiyya tabana domin girmama wadanda suka rasa rayukansu a lokacin wani hari da aka kai a Cocin St. Francis Catholic a garin Owo.
A ranar 5 ga Yuni ‘yan bindiga suka kai hari a cocin inda aka tabbatar mutuwar mutum 40 yayin da sama da mutum 120 kuma suka samu raunuka.
(NAN)