✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Kuje: ’Yan sandan sun damke fursunan da ya tsere a Binuwai 

Fursunan ya ce yana jiran shari'a kan zargin kashe budurwarsa.

Rundunar ’Yan Sandan jihar Binuwai a ranar Alhamis ta ce jami’anta sun damke wani Ebube Igwe Jude, wanda ya tsere daga gidan yarin Kuje bayan da ’yan ta’adda suka fasa gidan yarin.

Kakakin rundunar, SP. Catherine Anene, a cikin wata sanarwa, ta ce jami’an tsaro da aka tura domin binciken lamarin sun kama wani a George Akume Way, Wurukum a Makurdi.

“A ranar 19/7/2022 da misalin karfe 3 na rana, an samu labarin wani Ebube Igwe Jude, wanda aka gani a Makurdi bayan tserewarsa daga Gidan Yarin Kuje.

“A yayin bincike, ya amsa cewa ya tsere daga gidan yarin na Kuje. Ya kuma kara da cewa shi fursuna ne da ke jiran hukunci kan kisan da ya shafi budurwarsa,” in ji Anene.

Kakakin ta kara da cewa rundunar ta fara shirin mika fursunan zuwa ga Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya domin daukar matakan da suka dace.