✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kwashe dalibai zuwa barikin soji bayan harin FCFM

Sa’o’i kadan bayan Fadar Shugaban Kasa ta ce babu sulhu da ’yan bindiga

Sojoji sun kwashe daliban Kwalejin Horon Samar da Na’urorin Kula da Gandun Daji (FCFM), Afaka, Kaduna zuwa barikin soji bayan ’yan bindiga sun kai hari tare da yin garkuwa da wasu daliban kwalejin.

Bayan harin na garin Kaduna ne a safiyar Juma’a sojojin Rundunar Sojin Kasa ta 1 suka kwashe ragowar daliban zuwa cikin Barikin Sojin Ribadu da ke garin.

An sace daliban ne washegarin sanarwar Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Bagana Monguno cewa gwamnati ba za ta tattauna ba da ’yan bindiga.

Majiyarmu ta soji ta ce dakarun Rundunar Sojin Sama da Sojin Kasa sun fatattaki maharan bayan sun yi artabu da su a lokacin da  suka kai farmaki da asubahin ranar Juma’a.

Ta ce sojojin sun samu kubutar da wasu daga cikin dalibai, amma ’yan bindigar sun tafi da wasu daga cikinsu da ba a tantance yawansu ba.

Wasu majiyoyi na cewa dalibai mata ne maharan suka yi awon gaba da su.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda reshen Jihar Kaduna, Muhammad Jalige ya shaida wa Aminiya cewa: “An yi garkuwa da su ne a cikin dare, amma babu bayani game da yawansu, kuma ba zan iya cewa ba ko dukkansu mata ne”.

Ya kuma ce suna aiki tare da sojoji wajen bin sawun masu garkuwar da kuma kubutar da daliba.

Da yake tabbatar da garkuwa da daliban,  Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ya ce sun riga sun isa kwalejin don tantance hakikanin abun da ya faru.

Bayan luguden wuta da maharan suka yi da tsakar dare sannan suka yi awon gaba da daliban, an wayi garin Juma’a da ganin iyayen dalibai da mazauna sun yi dafifi a makarantar da ke cikin garin Kaduna.

Makwabtaka da sojoji
Mazauna sun tabbatar da jin karar hare-hare a cikin dare, amma sun dauka daga Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soji ta NDA ne.

Mando unguwa ce mai makwabtaka da NDA da Babban Filin Jirgin Sama na Kaduna a bangare guda, da kuma Barikin Sojin Sama da kuma Hedikawatar Runduna ta 1 ta Sojin daga daya bangaren.

Tuni jami’an tsaro suka isa kwalejin suka fara bincike yayin da jirgi ke shawagin gano inda aka bi da wadanda aka sacen.

Hari kan makarantu

Harin FCFM Afaka shi ne kusan na farko da aka kai wa wata makarantar gaba da sakandare inda aka yi garkuwa da dalibai.

An kai harin ne sa’o’i kadan bayan Shugaba Buhari ya ba wa Manyan Hafsoshin Tsaro wa’adin mako shida, wato kafin faduwar damina, su magance matsalar ’yan bindiga da ta addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ya kuma umarci jami’an tsaro su harbe duk wanda aka gani dauke da bindiga ba bisa ka’ida ba.

Ko a ranar Alhamis sai da Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Bagana Monguno, ya shaida wa Babban Ya kan Tsaron Kasa cewa gwamnati ba za ta tattauna ba da ’yan bindiga —ragargazar su za ta yi, in ya so, in sun ga uwar bari za su mika wuya.

 

Shin Jangebe ne na karshe?

Gabanin harin, Buhari ya yi alkawarin cewa sace dalibai mata 279 da ’yan bindiga suka yi a makarantar sakandaren GGSS Jangebe, Jihar Zamfara, shi ne zai zama karon karshe da aka yi garkuwa da dalibai a Najeriya.

Sai dai ko a ranar Laraba sai da daliban wata makarantar Sakandare suka tsallake rijiya daga hannun ’yan bindiga da suka kai hari a Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.

Harin da ya sa daliban tsere domin kubutar da rayukansu yayin da suke tsaka da daukar darasi, an kai shi ne sa’o’i kadan bayan Manyan Hafsoshin Tsaro sun ziyarci Jihar domin shawo kan matsala ayyukan ’yan bindiga.

Bayan bayan tafiyarsu da sa’o’i, Gwamna Bello Matawalle ya sanar cewa Buhari ya ba wa ’yan bindiga wata biyu su mika wuya ko su yaba aya zaki.

A yayin jawabin ne kuma ya sanar cewa Buhari ya ba da umarnin tura karin sojoji 6,000 zuwa jihar domin fatattakar ’yan bindiga.