Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce har yanzu akwai mutane da dama da ke cikin jirgin kasan da aka kai wa hari daga Abuja zuwa Kaduna ranar Litinin da ba ta san inda suka shiga ba.
Aminiya ta ruwaito yadda ’yan ta’adda suka dasa wa jirgin bam a kan titinsa kuma ya taka, bayan ya bar Abuja da niyyar zuwa Kaduna.
- Na kadu matuka da harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna — Buhari
- Hisbah ta kama kwalaben burkutu 96 a Jigawa
Daga bisani kuma maharan sun bude wa fasinjojin jirgin wuta, suka kashe wasu sannan suka yi awon gaba da mutanen da ba a san adadinsu ba.
Amma a cewar Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce sun gano gawarwakin mutum takwas da aka kashe, yayin da mutum 26 da suka samu raunuka kuma suna can a asibiti suna samun kulawa.
Sai dai sabanin adadin da ake yadawa, Kwamishinan ya ce yawan fasinjojin da suka samu daga Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Nejeriya (NRC), ya nuna mutum 362 ne suka hau jirgin.
Ya ce, “Kamar yadda takardun da muka samu suka nuna, mutum 398 ne suka sayi tikitin jirgin, amma mutum 362 ne kawai aka iya tantance sun hau shi.
“Amma jerin sunayen bai kunshi ma’aikatan NRC na cikin jirgin ba.
“Jami’an tsaro sun tabbatar da rasuwar mutum takwas, 26 kuma suka jikkata yayin harin.
“Amma muna ci gaba da binciken ragowar fasinjojin da ke kan jirgin, amma har zuwa yanzu ba mu san inda suke ba,” inji Kwamishinan.
Sai dai ya ce ana ci gaba da cigiyar mutanen ko za a samu a ceto su.