✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harin Boko Haram: Zulum ya koma Borno a jirgin yaki

Gwamna Zulum ya katse tarukan da yake halarta a Abuja bayan harin Boko Haram a Hawul.

Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum, ya katse ziyararsa Abuja a ranar Lahadi, tare da daukar jirgin yaki ya tafi yankunan da Boko Haram ta kai wa hari a Karamar Hukumar Hawul da ke jihar.

A ranar Alhamis ne Zulum ya je Katsina, daga nan ya tafi Abuja domin halartar wasu tarurruka, amma katse ya koma jiharsa sakamakon harin da kungiyar ta kai a ranar Asabar.

Tashan Alade, Shafa, Azare, Sabon-Kasuwa da Debro, na daga cikin yankunan da Boko Haram din ta kai hari.

Mayakan sun kashe mutum 3, tare da kone shaguna, wuraren ibada, makarantu, sannan kuma suka yashe kayan abincin da manoma suka girbe.

Gwamna Zulum ya ziyarci Yimirshika, Azare, Sabon-Kasuwa da Shafa, don gane wa idonsa irin barnar da ’yan ta’addar suka yi, kuma nan take ya umarci a sake gina caji ofis, kasuwa, da wasu wuraren da aka kone.

Ya kuma ba da umarnin a kawo motocin sintiri da za su taimaka wa ’yan banga da ke yankunan da abun ya shafa.

Zulum ya ce ya kadu matuka ganin yadda aka yi wa jama’a barna, domin a cewarsa rayuka da dukiyoyin al’umma su ne abu mafi muhimmanci a wajensa.

Ya shaida wa ’yan jarida cewa ziyarar tasa karfafa gwiwa da jaje ne ga mutanen yankin.

Gwamnan ya samu rakiyar Mataimakin Gwamna Umar Usman Kadafur, tsohon Mataimakin Gwamna Usman Mamman Durkwa, Sanata mai wakiltar Kudancin Borno Sanata Mohammed Ali Ndume, Kwamishinan Ayyuka da gyare-gyare Injiniya Mustapha Gubio da Kwamishinan Noma Injiniya Bukar Talba.