✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Boko Haram: Sojoji na cikin shirin ko-ta-kwana

Hedikwatar tsaro ta ce ta shirya tsaf domin dakile harin Boko Haram a Abuja

Rundunar Tsaro ta Najeriya ta ce tana cikin shirin ko-ta-kwana domin dakile yunkurin harin kungiyar Boko Haram a Birnin Tarayya Abuja.

Hedikwatara Tsaro ta Kasa ta ce dakarunta na yin sintiri a Abuja da sauran jihohi domin dakile duk wata barazanar tsaro a fadin Najeriya.

Ta sanar da hakan ne bayan wani rahoto da hukumar yaki da fasakwauri kasa ta fitar cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun shigo Abuja da nufin kai hare-hare a wasu wurare biyar.

Rohoton hukumar ya ce mayakan kungiyar sun yi sansanoni da Dajin Kunyan da Dajin Kwaku a Abuja; sai kuma Dajin Unaisha da ke Jihar Nasarawa da kuma Dajin Gegu da ke Jihar Kogi.

Kakakin Rundunar Tsaro, Manjo Janar John Enenche, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi ya ba bukaci ‘yan Najeriya su kwantar da hankalinsu tare da ba su tabbacin cewa rundunar ta riga da dauki matakan ta kuma sha gaban maharan.

“Sojoji da sauran hukumoin tsaro na aiki tare musamman wajen tara bayanan sirri suna kuma ba wa al’umma tabbacin cewa matakan dakile barazana na kan aiki. Ana shawartar jama’a su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin bin doka da oda.”

Enenche ya ce hukumomin tsaro ba za su kakkauta ba wajen fatattakar ‘yan ta’adda, han sai an samu cikakken lumana a fadin Najeria.

Kazalika Rundunar ‘Yan Sandan Abuja ta ba wa al’umma tabbacin cewa tana aiki ka’in da na’in domin yakar manyan laifuka a Abuja.

Kakakinta, DSP, Anjuguri Manzah, ya ce rundunar na aikin hadin gwiwa domin karkafa tsaro a fadin Abuja.